Jagoran 'Yan Bindiga Ya Tura Sako ga Gwamnati, Ya Fadi Matsayar Sulhun da Aka Yi a Katsina
- Tubabbun 'yan bindiga sun nuna damuwa kan yadda gwamnati ta yi watsi da su bayan cimma yarjajeniya a wasu yankunan jihar Katsina
- Wani tsohon jagora a dabar 'yan bindiga, Wada Yellow Musawa ya jaddada cewa ba zai koma aikata ayyukan ta'addanci ba duk da barnar da aka masa
- Ya tabbatar da cewa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a karamar hukumar Musawa tana nan daram duk da sababbin hare-haren da aka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Wani jagoran dabar ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Musawa, Wada Yellow Musawa, wanda ya tuba ya ajiye makamansa, ya ce yarjejeniyar zaman lafiya na nan daram.
Wada ya bayyana cewa yarjejeniyar zaman lafiya da ke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga daban-daban da mazauna yankin tana nan tana aiki duk da sababbin hare-haren da ake samu.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Matsalar da aka samu a sulhun Amurka da Iran ya rusa mafarkin 'yan Najeriya

Source: Original
Daily Trust ta tattaro cewa a wata hira ta wayar tarho, ya danganta sababbin hare-haren da wasu ‘yan bindiga da suka gudo daga Zamfara, inda ya ce suna shigowa yankin Musawa domin satar shanu.
Tubabbun 'yan bindiga sun fadi damuwarsu
Sai dai Wada ya koka kan cewa an janye tallafin da suke samu daga hukumomin gwamnati, lamarin da ya rage karfinsu wajen kare al'umma daga hare-haren.
Ya ce a baya-bayan nan sun tare wasu ‘yan bindiga, inda suka yi artabu da su suka kashe da dama, yayin da wasu suka tsere.
Ya kara da cewa daga baya ‘yan bindigan sun sake dawowa da karfi, inda suka kai masu harin ramuwar gayya.
Barnar da aka yi wa Wada Yellow
A cewarsa, harin ya yi sanadin rasuwar mahaifinsa da matar dan uwansa, sannan an kona gidansa tare da sace masa shanu, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kutsa cikin otal, sun sace shugaban karamar hukuma a Najeriya
“Ba zan janye daga yarjejeniyar zaman lafiya ba, domin na rantse ba zan koma harkar ‘yan bindiga ba. Amma dole na koma cikin daji saboda rashin tsaro, sannan tallafin da muke samu a baya ya daina zuwa,” in ji shi.
Duk da irin asarar da ya yi, Wada Yellow ya jaddada cewa yana nan kan bakansa na ci gaba da zaman lafiya.

Source: Facebook
Kungiyar MACBAN ta gano matsala
Haka zalika, shugaban kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) ta kasa reshen Musawa, Lawan Ibrahim Ribeji, ya ce yawaitar shigowar ‘yan bindiga daga Zamfara ya zama abin damuwa.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar zaman lafiyar tana aiki yadda ya kamata kafin wasu miyagun yan bindiga suka fara kai wa Wada Yellow hari.
Ribeji ya kara da cewa duk da kokarin shugaban karamar hukuma, halin da ake ciki yanzu na bukatar karin matakin tsaro mai karfi.
An yi artabu tsakanin 'yan bindiga a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga akalla 40 sun bakunci lahira yayin da fada ya kaire tsakaninsu a wasu yankuna a jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin 'yan bindigan ya ta tilasta wa al’ummar fiye da kauyuka 10 dakatar da sallar Juma’a don tsaretar da rayukansu.
Mazauna garin Dangani da ke karamar hukumar Musawa, sun ce ‘yan bindiga da dama sun kai farmaki da rana jim kadan kafin lokacin sallar Juma’a.
Asali: Legit.ng