Yakin Iran da Isra'ila: Tinubu Ya Dauko Hanyar Rage wa yan Najeriya Radadin Rikicin

Yakin Iran da Isra'ila: Tinubu Ya Dauko Hanyar Rage wa yan Najeriya Radadin Rikicin

  • Shugaba Bola Tinubu ya dauko hanyar saukaka wa yan Najeriya game da rikicin Iran da Isra'ila da ake yi a yanzu
  • Tinubu ya umarci jami’an tattalin arziki su samar da matakan rage radadin da rikicin Gabas Ta Tsakiya
  • Ya ce farashin mai da tsadar rayuwa sun karu sakamakon rikicin, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta nemo mafita mai dorewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yenagoa, Bayelsa - Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin samar da hanyoyin rage tasirin raɗaɗin rikicin Gabas ta Tsakiya ga ƴan Najeriya

Tinubu ya bukaci jami’an tattalin arzikin Najeriya da su gaggauta fito da matakan da za su rage wa talaka radadin da rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya ya jefa shi a ciki.

Tinubu zai taimaka wa yan Najeriya kan radadin da suke ciki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X yayin ziyarar Tinubu a jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Sojoji sun ba hammata iska yayin ziyarar Tinubu a Bayelsa, bidiyo ya fito

Tinubu ya damu kan rikicin Iran da Isra'ila

Shugaba Tinubu ya bayar da wannan umarni ne yayin wata liyafa da aka shirya masa a birnin Yenagoa, bayan ya kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Douye Diri ya samar a Jihar Bayelsa.

Tinubu ya dora wa Ma’aikatar Kudade da ta Tsare-tsare, tare da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther Walson-Jack, nauyin duba hanyoyin da za a saukaka wa ‘yan kasa halin matsin tattalin arziki.

Shugaban ya amince cewa lallai rikicin duniya ya janyo tsadar rayuwa, musamman ta fuskar farashin man fetur da ke addabar jama’a.

“Ina jin koke-kokenku ta kowane bangare na tattalin arziki. Farashin mai na ratsawa, amma dole mu yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya."

- Bola Tinubu.

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyuka a Bayelsa
Shugaba Bola Tinubu, Goodluck Jonathan da mai dakinsa yayin ziyara a Yenagoa, Bayelsa. Hoto: @Dolusegun.
Source: Twitter

Tabbacin da Tinubu ya ba yan Najeriya

Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa mai kula da jin dadin jama’a ce, kuma za ta zauna da masana domin fito da lissafin da zai saukaka wannan nauyi da ya danne kafadar talaka.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Tinubu ya nuna kukan dadi 'yan Najeriya ke yi

Haka zalika, ya jaddada aniyar jam’iyyar APC na inganta jin dadin jama’a ta hanyar ayyukan raya kasa da ke taba rayuwar talaka kai-tsaye.

A yayin ziyarar, Shugaban ya kaddamar da wasu gagaruman ayyuka a jihar, ciki har da tashar samar da wutar lantarki ta ‘gas’ mai karfin megawat 60 a kauyen Elebele, da gadar Angiama zuwa Oporoma mai tsawon mita 630, da kuma wata sabuwar babbar hanyar shiga birnin Yenagoa.

Tinubu ya yaba wa Gwamna Diri kan yadda yake tafiya tare da tsarin ‘Sabunta Fata’ na Gwamnatin Tarayya, inda ya bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin jiha da tarayya shi ne sirrin kawo ci gaba cikin hanzari.

Tinubu ya tattauna da kasashe kan tsaro

Mun ba ku labarin cewa jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya ya ce shugaba Bola Tinubu na tattaunawa da kasashe domin nemo mafita ga matsalolin tsaro.

Jimoh Ibrahim ya bayyana cewa Najeriya ba ta dogara da kasa guda wajen magance matsalolin tsaro ba, yana mai cewa ana maraba da agaji daga kasashe.

A bayaninsa a Amurka, ya ce Najeriya kasa ce mai cikakken iko da za ta cigaba da zama daya duk da kalubalen da ta ke fama da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.