Kashe Kashe a Najeriya Ya Damu Atiku Sosai, Ya Yaba wa Gwamnatin Amurka
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan hare-haren ta’addanci da ke faruwa a Najeriya,
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa matsalar tsaro na barazana ga haɗin kai, zaman lafiya da dorewar ƙasa baki ɗaya
- Ya buƙaci gwamnati ta ƙara ƙaimi da haɗin gwiwa wajen kare rayuka da dukiyoyi, yana jaddada cewa nauyin farko na kowace gwamnati shi ne tabbatar da tsaro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da yawan hare-haren ta’addanci da ke faruwa a sassan Najeriya.
Atiku ya yi gargadin cewa wannan yanayi na iya kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa tare da neman gwamnati ta dauki mataki.

Source: Getty Images
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana hare-haren a matsayin abin takaici da kuma abin da bai dace ba.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan majalisa ya ƙare kansa kan zargin fitar da bayan sirrin Najeriya ga ƙasashen waje
Atiku ya koka kan rashin tsaron Najeriya
Atiku ya bayyana cewa bai kamata irin waɗannan ayyuka su zama abin da ke bayyana halin al’ummar Najeriya ba.
Ya kuma jajanta wa waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda abin ya shafa, tare da kira ga hukumomi da su ɗauki matakai masu ƙarfi da haɗin gwiwa domin shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a ƙasar.
Atiku ya ce:
"Babban alhakin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyi. Don haka ya zama dole a ɗauki matakan gaggawa, haɗin kai da ƙuduri wajen magance wannan ƙalubale da dawo da amincewar jama’a."
Atiku ya kuma yaba wa rawar da ƙasashen waje ke takawa, musamman Amurka, wajen tallafa wa Najeriya a yaƙi da ta’addanci, yana mai cewa irin wannan haɗin gwiwa na duniya na da matuƙar muhimmanci.

Source: Facebook
Yadda Boko Haram ta kai hari a Borno
Wannan bayani na Atiku ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sababbin hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da Borno, inda aka kai hari kan sansanin sojoji a Benisheikh, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’ai ciki har da wani janar.
A lokacin bikin Easter, hare-hare sun kuma faru a Kaduna da Benue, inda aka kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu, lamarin da ya ƙara jefa al’umma cikin fargaba.
An kuma samu hare-hare a wasu yankuna kamar Katsina da Kebbi da kuma Kwara, inda aka yi asarar rayuka da lalata dukiyoyi a hare-haren ‘yan bindiga da ake zargin sun kai.
Duk da wannan yanayi mai tsanani, Atiku ya nuna ƙwarin gwiwa cewa Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen, inda ya ce Najeriya za ta ci gaba da kasancewa, kuma da haɗin kai za mu yi nasara.
Atiku ya kulla yarjejeniya da kamfanin Amurka
Mun ba ku labarin cewa Atiku Abubakar ya rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar Dala miliyan 1.2 da kamfanin kamun kafa na Amurka.
Yarjejeniyar na da nufin ƙarfafa sunansa da dangantakarsa da hukumomin Amurka kafin zaɓen 2027 da za a yi a Najeriya.
Ana ganin matakin na da alaƙa da fafatawar tikitin shugaban ƙasa a jam’iyyar hamayya ta ADC da za a yi nan gaba kaɗan.
Asali: Legit.ng
