'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake da Jami'an Tsaro bayan Ya Dawo Najeriya
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika yayin wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Imo ta tarayyar Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka wani basarake tare da jami'an tsaro na 'yan sanda yayin harin da suka kai masu
- Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta bayyana cewa an tura karin jami'ai domin cafko mutanen da suka aikata danyen aikin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Imo - 'Yan bindiga dauke da makamai sun hallaka wani basarake da jami'an 'yan sanda a jihar Imo.
'Yan bindigan sun kashe basaraken na mazaɓar Ochia Awarra Ohaji, Ochia Paulinus Ekwueme, har lahira a kan iyakar kauyukan Assa da Ochia, da ke ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema a jihar Imo.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa 'yan bindigan sun kashe basaraken ne a ranar Juma'a, 10 ga watan Afirilun 2026.
'Yan bindiga sun yi barna a Imo
Wani abin ban takaici shi ne yadda 'yan bindigan suka harbe wasu jami’an sanda da ke cikin ayarin motocinsa, inda aka yi zargin cewa maharan sun ƙone gawarwakin nasu bayan kashe su.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Imo, DSP Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ba da tabbacin cewa an riga an tura jami’an tsaro kuma yankin yana cikin kwanciyar hankali.
Yadda aka kashe basarake
Wata majiya daga ƙauyen, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa basaraken ya dawo jihar Imo ne daga ƙasar waje a ranar Juma’a, sai dai cikin rashin sa’a ya riga mu gidan gaskiya a ranar da ya dawo.
An yi wa basaraken da jami’an tsaron kwanton-bauna ne a kan iyakar kauyukan Assa da Ochia.
Majiyar ta ce ba za ta iya tabbatar da adadin jami’an tsaron da abin ya shafa ba, amma bayanan da ke akwai sun nuna cewa bayan kisan, an cinnawa gawarwakinsu wuta.

Kara karanta wannan
An yi rashi: Yadda 'yan ta'addan ISWAP suka kashe babban Janar da sojoji 17 a Borno
"Hari ne da aka tsara aka kuma aiwatar da shi cikin kwarewa; lallai wani ne ya bayar da bayanin cewa zai dawo ƙauyen a yau."
“Sarkinmu ya isa Owerri ne a yau daga ƙasar waje, yana kan hanyarsa ta zuwa ƙauye aka kai masa hari aka kashe shi. An shaida mana cewa ’yan bindigar sun ƙona su. Daukacin yankin Ohaji ya shiga cikin makoki."
- Wata majiya

Source: Original
'Yan sanda sun yi bayani
A nasa ɓangaren, kakakin ’yan sandan, Okoye, ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Audu Garba Bosso, ya riga ya ba da umarnin tura jami’an bincike na musamman zuwa daukacin ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema domin tabbatar da tsaro.
"Haka ne, ina da masaniya kan lamarin amma ba ni da cikakken bayani a yanzu, don haka ba zan iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasu ba."
“Tuni dai kwamishinan ’yan sanda na jihar Imo, Audu Garba Bosso, ya ba da umarnin tura tawagar jami’an rundunar don fara bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan danyen aiki."
“Haka kuma, CP ya tura jami’an tsaro isassu domin kamo masu kisan. Kuma ina ba ku tabbacin cewa za mu kamo su duk inda suka buya.”

Kara karanta wannan
Rundunar sojoji ta tabbatar da kashe jami'anta, an ji abin da ta ce kan kisan Janar
- DSP Henry Okoye
'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka bayin Allah yayin wani hari a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun hallaka aƙalla mutane takwas yayin da wasu huɗu suka ji rauni a harin da suka kai kauyen Vole da ke gundumar Kwatas a karamar hukumar Bokkos.
Tsagerun 'yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 8:00 zuwa 9:00 na dare inda suka yi ta'asa kafin su tsere.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
