Abin Tsausayi: An Shiga Firgici da Aka Gano Gawarwakin Mutane Sama da 60 a Jihar Neja

Abin Tsausayi: An Shiga Firgici da Aka Gano Gawarwakin Mutane Sama da 60 a Jihar Neja

  • Ana ci gaba da samun bayanai daga mummunan harin da yan bindiga suka kai yankin karamar hukumar Shiroro a Neja ranar Talata da ta wuce
  • Rahoto ya nuna cewa zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane akalla 61, wadanda suka kunshi jami'an tsaro da fararen hula
  • Mazauna yankin da abin ya shafa sun fara barin gidajensu bayan samun rahoton cewa 'yan bindiga na shirin sake kawo hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - An gano aƙalla gawarwaki 61 na jami’an tsaro da fararen hula da aka kashe a harin ‘yan bindiga da aka kai ranar Talata a garuruwan Bagna da Erena da ke ƙaramar hukumar Shiroro, jihar Neja.

Mazauna yankin sun ce an kwaso gawarwakin ne a dazukan da ke kusa kwanaki kadan bayan harin yan bindigar, inda aka binne fararen hula a garin Erena.

Kara karanta wannan

Rikici ya tsananta: Harin Isra'ila kan motocin agaji ya girgiza Lebanon

Jihar Neja.
Taswirar jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa yau Juma'a, ta ce an kai gawarwakin jami’an tsaro zuwa dakin ajiye gawa na asibitin gwamnati da ke Minna.

An kashe jami'an tsaro da fararen hula

Wani mazaunin Erena wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Daga cikin waɗanda aka kashe akwai ‘yan banga, jami’an hukumomim tsaro daban-daban da kuma bayin Allah fararen hula

Sai dai rahotanni sun nuna cewa rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja ta tabbatar da mutuwar ‘yan banga uku kacal.

Daya daga cikin waɗanda suka mutu shi ne shugaban ‘yan bangar yankin mai suna, Manga, wanda aka ceto da rai bayan ya ji rauni a artabu, amma daga bisani ya rasu sakamakon raunukan harbin bindiga.

Martanin mazauna yankin

Mazauna yankin sun yaba da kokarin jami’an tsaro da suka kai dauki, inda suka ce daga karshe sun fatattaki ‘yan bindigar.

Sai dai sun zargi gwamnati da gazawa wajen daukar mataki tun da wuri duk da bayanan sirri da aka samu kafin harin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bauchi ta dauki mataki bayan gano hanyoyin samun kudin 'yan bindiga

Bayan harin, fargaba ta karu a yankunan da ke kusa, inda a ranar Alhamis, mazauna yankin Bassa suka fara tserewa daga gidajensu bayan fara jita-jitar cewa za a sake kawo masu hari.

Gwamnan Neja.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago yayin jagorantar taron tsaro a Minna Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

Mutane sun fara barin gidajensu

An ga mata da yara suna kokarin tserewa ta cikin kwale-kwale, a daidai lokacin da ake hasashen daruruwan mutane sun rasa matsugunansu a yankin.

Rahoto ya nuna cewa a yanzu suna samun mafaka a makarantar firamare ta Zumba da sauran wurare da suka fi tsaro a Shiroro, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Wani manomi, Rabiu Iliyasu, ya ce:

“Mun ga jiragen sama suna kai hare-hare a kusa da mu. Jami’an tsaro suka janye domin kauce wa kuskure, mu kuma muka gudu saboda babu kariya.”

Shi ma wani mazauni, Suleiman Abdullahi, ya ce jita-jitar taruwar ‘yan bindiga ne ya sa jami’an tsaro suka shawarci mutane su boye ko su fice daga yankin.

Boko Haram ya tarwatsa gada a jihar Neja

An ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun yi amfani da bam wajen tarwatsa wata gada mai muhimmanci a hanyar Wawa zuwa Guffanti a jihar Neja.

Kara karanta wannan

DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya

Wannan hanya, wadda ta kasance mai cike da hada-hadar mutane da ababen hawa, ta ratsa har ta cikin dajin Kainji Lake National Park.

Mazauna yankin sun bayyana cewa wannan harin da ya tarwatsa gadar ya nuna ƙudurin 'yan ta'addan na durƙusar da tattalin arziƙin jama'ar da ke rayuwa a garuruwan wajen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262