Gwamnatin Bauchi Ta Dauki Mataki bayan Gano Hanyoyin Samun Kudin 'Yan Bindiga
- Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki matakin rufe wasu kasuwanni domin yaki da matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- A cikin sanarwar da aka fitar, an bayyana cewa an rufe kasuwannin shanu guda hudu 25 a kananan hukumomi hudu
- An umarci shugabannin hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da an sanya ido don ganin an aiwatar da umarnin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi: Gwamnatin jihar Bauchi ta rufe kasuwannin shanu guda 25 a fadin ƙananan hukumomi huɗu saboda matsalar 'yan bindiga.
Gwamnatin ta rufe kasuwannin a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin dakile hanyoyin samar da kuɗaɗe da kayan aiki ga 'yan bindiga da ke addabar jihar.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan Bauchi shawara ta musamman kan yada labarai, Mukhtar Gidado, ya aka fitar ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
Gwamnatin Bauchi ta rufe kasuwanni
Mukhtar Gidado ya ce Gwamna Bala Mohammed ne ya amince da wannan shawara, wadda ta shafi kasuwanni a ƙananan hukumomin Alkaleri, Bauchi, Kirfi, da Tafawa Balewa, jaridar The Cable ta kawo rahoton.
"An ɗauki wannan mataki ne domin magance matsalolin tsaro da suka taso sakamakon amfani da waɗannan kasuwanni wajen tallafawa manyan laifuffuka."
"Da suka haɗa da satar shanu, kisan kai, garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, karɓar kuɗaɗen haraji ta ƙarfin tsiya, sauƙaƙa musayar makamai, da yaɗa kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya da sauran su.”
“Waɗannan kasuwanni, yayin da suke ci gaba da aiki, sun zama wuraren da masu aikata laifuffuka ke fakewa suna satar dabbobi, tsoratar da ’yan kasuwa, da kuma dagula hanyoyin samar da abinci."
"Wanda hakan ke janyo babbar asara ga tattalin arziƙi lamarin da gwamnati ke kallo a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, kuma barazana ce ga rayuwar al’ummar da ke maƙwabtaka da wuraren."
“Duk da cewa wannan mataki na ɗan lokaci ne kuma zai ci gaba da aiki har sai an samu gagarumin ci gaba a fannin tsaro, an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da an bi wannan doka yadda ya kamata.”
- Mukhtar Gidado

Source: Original
Wadanne kasuwannin shanu aka rufe?
Kasuwannin da abin ya shafa sun haɗa da guda 14 a ƙaramar hukumar Alkaleri, Alkaleri, Mansur, Futuk, Yalo, Gwana, Yalon Gurza, Kuka, Rimi, Pali, Bokwas, Kwaimawa, Mai Ari, Gajin Duguri, da Maina Ma’aji.
A ƙaramar hukumar Kirfi, kasuwannin sune: Lariski Bara, Sharfuri (kasuwar dare), Cheledi, da Boli.
A ƙaramar hukumar Tafawa Balewa an lissafa kasuwanni biyar, Burga, Bununu, Ball, Kulumbo, da Zwall.
A ƙaramar hukumar Bauchi kuwa, fitacciyar kasuwar shanu ta Liman Katagum ita ma abin ya shafa.
A cewar sanarwar, an umarci shugabannin ƙananan hukumomi da iyayen ƙasa da suka haɗa da sarakuna, hakimai, da dagattai da su wayar wa mazauna yankunansu kai kan wannan umarni, sannan su tabbatar da ana sanya ido sosai wajen aiwatar da shi.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.
'Yan bindigan sun hallaka akalla mutane takwas a hare-haren da suka kai a kauyen kauyen Vole da ke gundumar Kwatas a karamar hukumar Bokkos.
Shugaban majalisar matasan jihar Plateau (PYC) na reshen Bokkos, Dakol James, ya ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 8:00 zuwa 9:00 na dare.
Asali: Legit.ng

