Yan Bindiga Sun Kona Coci da Masallaci bayan Hallaka Musulmi da Kirista 24

Yan Bindiga Sun Kona Coci da Masallaci bayan Hallaka Musulmi da Kirista 24

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane 24 sun mutu a hare-haren yan bindiga a wasu kauyukan jihar Kebbi
  • Cocin Katolika na Kontagora ya ce wadanda aka kashe sun hada da Musulmi da Kiristoci, tana mai bayyana lamarin a matsayin bala’i
  • Daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu, inda sama da 400 ke neman mafaka, yayin da aka roki Bola Tinubu yakawo dauki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Cocon Katolika na Kontagora ta bayyana damuwa kan karuwar hare-haren yan bindiga a jihar Kebbi kan al'ummomin Kirista da Musulmi.

Cocin ya ya ce akalla mutane 24 sun mutu a wani hari da aka kai a ranar bikin 'Easter' a kauyen Debe da ke karamar hukumar Shanga.

Yan bindiga sun kashe al'umma a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi da ake fama da hare-haren yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda yan bindiga suka kashe Musulmi, Kirista

Harin na baya-bayan nan ya biyo bayan wasu hare-hare da ake kai wa a yankunan iyaka tsakanin Kebbi da Niger, inda ‘yan bindiga ke kai farmaki kan kauyuka da dama, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Lamari ya sauya: Ƴan bindiga sun bukaci daruruwan shanu, dabbobi a matsayin haraji

Majiyoyin tsaro sun ce ana zargin maharan sun fito ne daga dazukan Wawa da ke karamar hukumar Borgu a Niger.

Rundunar ‘yan sanda ta Kebbi ta tabbatar da tura jami’an tsaro, sojoji da masu gadin sa-kai domin dawo da doka da oda a yankin.

An kashe Musulmi, Kirista bayan kona wuraren ibada
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Coci ya fadi yadda aka kashe Musulmi, Kirista

A cikin wata sanarwa da aka fitar a Yauri, cocin ya ce maharan sun kai hari da misalin karfe 5 na yamma ranar 5 ga Afrilun 2026, inda suka kashe mutane da dama tare da lalata dukiyoyi.

Ya ce adadin wadanda suka mutu ya kai 24, sabanin rahoton farko da ya ce mutum hudu ne kawai suka rasu, cewar Channels TV.

Cocin ya bayyana cewa wadanda aka kashe sun hada da Musulmi, Kiristoci da masu bautar gargajiya, tana mai cewa wannan bala’i ne da ya shafi kowa da kowa.

Yan bindiga sun kona masallaci, coci

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kona cocin St. Mary, masallaci, gidaje da shaguna, inda suka fi kai hari kan maza da matasa.

Kara karanta wannan

Bayan Iran, gwamnatin Trump ta juyo Najeriya, ta yi gargadi kan tsaro

Harin ya bazu zuwa wasu yankuna makwabta kamar Binuwa da Kalkame, inda aka lalata kasuwanni da ma gidan sarki.

Bayan harin, daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu, inda mutane 491 ke samun mafaka a cocin St. Dominic da ke Yauri.

Cocin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta Kebbi su dauki matakin gaggawa domin dawo da tsaro da bai wa wadanda suka gudu damar komawa gidajensu.

Ya kuma roki Bola Tinubu da hukumomin gwamnati su dauki matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro a Kebbi

A baya, kun ji cewa Gwamna Nasir Idris ya tabbatar da kisan sojoji tara da dan sanda daya bayan yan bindiga sun yi musu kwanton bauna a jihar Kebbi.

'Yan bindiga sun kona motocin sojoji guda biyu kurmus a yankin Shanga yayin da dakarun tsaron ke kokarin kare wani gidan kera gine-gine.

Gwamnatin jihar Kebbi ta yi alkawarin biyan kudaden maganin wadanda suka ji raunuka tare da tallafa wa iyalan jami'an tsaron da suka rasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.