Ana Jimamin Kisan Janar, 'Yan Bindiga Sun Sake Tafka Ta'asa a Jihar Plateau
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani kauye na karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau
- Tsagerun 'yan bindigan sun kai harin ne cikin dare inda suka kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- 'Yan bindigan sun kuma raunata mutane da dama a harin wanda suka kai a daren ranar Alhamis, 9 ga watan Afirulun 2026
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - 'Yan bindiga sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun hallaka aƙalla mutane takwas yayin da wasu huɗu suka ji rauni a harin da suka kai kauyen Vole da ke gundumar Kwatas a karamar hukumar Bokkos.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa harin ya auku ne a daren ranae Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026.
Harin ya faru ne kwana ɗaya bayan wasu makamantan hare-hare da aka kai a wani wurin hakar ma'adinai a ƙauyen Kok da ke gundumar Ropp, da kuma ƙauyen Chenye a gundumar Bachi da ke ƙananan hukumomin Barkin Ladi da Riyom, inda aka kashe mutane biyu.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
Yayin da yake tabbatar da harin na Vole, Shugaban majalisar matasan jihar Plateau (PYC) na reshen Bokkos, Dakol James, ya ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 8:00 zuwa 9:00 na dare, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Dakol James ya yi tir da harin, inda ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen wannan tashin hankali.
“Daukacin matasan Bokkos sun yi matuƙar takaici da yanayin tsaro. Har zuwa safiyar yau, ba a tura jami'an tsaro ko ɗaya don tantance halin da ake ciki ba. An kwashe kusan sa'o'i 12, amma ba mu ga wani jami'in tsaro ba."
- Dakol James
'Yan bindiga sun yi harbe-harbe
Haka zalika, wani jagoran matasa a Bokkos, Christopher Luka, ya ce ya fara jin ƙarar harbin bindiga ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, amma bai gano inda harbin yake fitowa ba a lokacin.
“Lokacin da na ji ƙarar harbin, na fara kiran wasu don jin daga inda harbin yake fitowa. Kafin hakan, yankin ya kasance cikin kwanciyar hankali."
“Ba a samu wani tashin hankali ba kwanan nan, don haka wannan harin ya zo mana da mamaki. Muna kyamatar harin da kuma rashin jami'an tsaro a wurin."
- Christopher Luka
Christopher Luka ya kara da cewa shugabannin matasa sun yi aiki tuƙuru don kwantar da hankulan mazauna yankin, inda suka buƙaci su natsu yayin da suke jiran daukar mataki daga jami’an tsaro.

Source: Original
An yi Allah wadai da harin
Shi ma a nasa ɓangaren, shugaban kungiyar Fulani ta Gan Allah (GAFDAN) na Bokkos, Saleh Adamu, ya yi Allah-wadai da harin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici.
“Na yi mamakin jin labarin harin, musamman ganin yadda al’ummar ke zaune cikin kwanciyar hankali. Ba a samu wani abu da zai janyo hakan ba."
“Mun sha gudanar da tarurruka, kuma zaman lafiya yana dawowa a hankali. Wannan ci baya ne mai ban takaici."
“Har yanzu ba mu san waɗanda ke da alhakin hakan ba. Muna buƙatar jami'an tsaro su bincika tare da kamo waɗanda suka aikata hakan domin fuskantar shari'a."
- Saleh Adamu
Ba a ji ta bakin jami'an tsaro ba
Ƙoƙarin tuntuɓar kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh, da kakakin ’yan sandan Jihar Plateau, SP Alabo Alfred, ya ci tura.
Mutanen biyu ba su amsa saƙonnin tambayar da aka aika musu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
'Yan bindiga sun kakaba haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa sun kakabawa wasu kauyuka a jihar Katsina domin k. Da su kai musu farmaki.
Yan bindiga sun bukaci wasu yan ƙauyuka a jihar Katsina da su biya haraji da dabbobi saboda gudun kai masu farmaki.
Maharan sun bukaci shanu 700 da tumaki 1,000 daga wasu kauyuka uku a karamar hukumar Kankia da ke Katsina, inda suka yi masu barazanar kai hari idan suka kasa ba da abin da suka nema.
Asali: Legit.ng


