Boko Haram: Tinubu Ya Fadi Abin da Zai Biyo bayan Kisan Janar a Borno
- Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sha alwashin murkushe ta’addanci bayan harin da ya kashe janar da sojoji a jihar Borno
- Shugaban ya bayyana haka ne bayan sojoji sun dakile farmakin ‘yan Boko Haram a Benisheikh, amma an yi asarar rayuka da dama
- Bola Tinubu ya bayyana cewa rashin babban jami'in sojin ba zai sare ayyukan rundunar sojin kasar nan ba wajen yakar yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa Najeriya za ta yi nasara a yaki da ta’addanci, bayan harin da ‘yan Boko Haram suka kai a jihar Borno.
Duk da rahotanni sun ce sojoji sun yi nasarar dakile harin, amma ya yi sanadin mutuwar Brigediya Janar Oseni Braimah da wasu sojoji.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook, Bola Tinubu ya ce wannan hari ba zai sace gwiwar gwamnati ba wajen kawo karshen rikicin da ya dade yana addabar Arewa maso Gabas.
Bola Tinubu ya yi magana kan kashe soja
Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar sojojin rundunar 29 Task Force Brigade karkashin Operation Hadin Kai, wadanda suka mutu a wani hari da aka kai sansaninsu a yankin Benisheikh da ke Borno. Ya kuma jajanta wa rundunar soji da iyalan wadanda suka rasu, yana mai cewa sadaukarwarsu ba za ta tafi a banza ba.
Shugaban ya yabawa jarumtar sojojin da suka fafata da ‘yan ta’adda har suka tilasta masu janyewa daga harin.

Source: Twitter
Ya ce rahotannin da ya samu sun nuna cewa sojojin Najeriya na ci gaba da kai hare-hare masu ta kasa da sama, inda suke kashe ‘yan ta’adda da dama da shugabanninsu.

Kara karanta wannan
Za a jika wa APC aiki, tsohon jagoran yakin neman zaben Tinubu a Zamfara ya koma ADC
A cewarsa, mayar da martanin da ‘yan ta’addan suka yi alama ce ta rashin karfinsu da matsin lamba da suke fuskanta.
Tinubu ya gargadi kafafen yada labarai
Tinubu ya kuma gargadi kafafen yada labarai da ‘yan kasa da kada su rika yaba wa ko nuna goyon baya ga hare-haren da ake kai wa sojoji, yana mai cewa sojoji jarumai ne da ya kamata a girmama su.
Ita ma hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bukaci ‘yan Najeriya da kafafen yada labarai su mutunta ka’idojin soja wajen sanar da mutuwar jami’ai, musamman kafin a sanar da iyalansu.
Daraktan ayyukan yada labaran tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya tabbatar da harin da aka kai a Benisheikh da 12.30 na dare, inda ‘yan ta’adda suka yi kokarin kutsawa sansanin soja. Ya ce sojojin karkashin jagorancin Brigediya Janar Braimah sun mayar da martani cikin jarumta da kwarewa, inda suka fatattaki maharan tare da tilasta masu janyewa cikin rudani. Onoja ya kara da cewa wannan hari alama ce ta karancin karfin ‘yan ta’adda bayan da suka sha kaye a hare-haren baya.
An kashe babban soja a Borno
A baya, mun wallafa cewa Birgediya janar Oseni Omoh Braimah da sojoji 17 ne suka rasa rayukansu yayin wani harin 'yan ta'addan ISWAP a Borno, lamarin da ya gigiita rundunar da mazauna jihar.
Sojojin sun rasu ne a hare-haren da ISWAP ta kai a sansanonin sojoji a Benisheikh a ƙaramar hukumar Kaga, da Ngamdu, da kuma garin Pulka da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Majiyoyi daga cikin garin Benisheikh da suka tabbatar da hain sun bayyana cewa maharan sun yi ta harbin sansanin sojin ba kakkautawa, lamarin da ya janyo asarar rayuka masu yawa.
Asali: Legit.ng

