Da Gaske an kai Hari Abuja bayan Gargadin Amurka? Gaskiya Ta Fito

Da Gaske an kai Hari Abuja bayan Gargadin Amurka? Gaskiya Ta Fito

  • An yada wani bidyo a kafafen sada zumunta, musamman X da ke nuna cewa an kai hari wasu yankunan birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis
  • Hakan na zuwa ne bayan kasar Amurka ta sanar da janye wasu ma'aitakanta da ke aiki a Abuja tare da gargadi kan zuwa wasu jihohin Najeriya
  • Sai dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta fito ta yi magana game da jita-jitar, haka zalika wasu mazauna yakunan da aka ambata sun magantu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta musanta wani bidiyo da ya bazu yana ikirarin cewa an kai harin ta’addanci a Abuja.

A bayanin da rundunar 'yan sandan ta yi, ta bayyana bidiyon a matsayin ƙarya da aka yada domin rudar da mutane game da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka kashe mutane 2,360 a Borno, Filato da wasu jihohin Najeriya

'Yan sandan Najeriya a bakin aiki a Abuja
'Yan sanda yayin samame a iyakokin FCT, Abuja. Hoto: FCT Police Command
Source: Facebook

Martanin 'yan sanda kan 'harin' Abuja

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilun 2026, rundunar ta ce babu wata matsalar tsaro a ko’ina cikin FCT.

“Bidiyon da ke yawo yana ikirarin harin ta’addanci a Abuja ƙarya ne,”

Inji sanarwar.

“Babu wata matsalar tsaro a ko’ina cikin FCT. Bincike ya nuna cewa an shirya sautin harbe-harbe ne aka ɗaura shi a kan wani bidiyo daban da ba su da alaƙa.”

Abin da aka fada a bidiyon

Legit Hausa ta rahoto cewa bidiyon da aka karyata, wanda Stephen Osemwegie ya wallafa a X ya yi iƙirarin cewa:

“Ana ta harbe-harbe sosai a Babban Birnin Tarayya na Najeriya,'

Bidiyon ya jawo damuwa a tsakanin mazauna birnin tarayya Abuja bayan ya bazu cikin sauri a shafukan sada zumunta a ranar Alhamis.

'Yan sanda na bincike kan bidiyon

Kara karanta wannan

Za a jika wa APC aiki, tsohon jagoran yakin neman zaben Tinubu a Zamfara ya koma ADC

Kwamishinan ’yan sanda ya bayar da umarnin a gudanar da binciken fasaha domin ganowa da kuma kama waɗanda suka kirkiro bidiyon domin tayar da firgici.

Baya ga haka, dakarun ’yan sanda sun buƙaci jama’a da su yi watsi da irin wannan bayani tare da daina yaɗa shi a kafafen sada zumunta.

Taswirar birnin tarayya Abuja
Taswirar birnin tarayya Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa shaidu daga mazauna yankin Katampe Extension sun nuna cewa wurin ya kasance cikin kwanciyar hankali a lokacin da aka wallafa bidiyon da kuma bayan haka.

Bugu da ƙari, babu wani rahoto daga ’yan sanda ko kuma sahihan kafafen yaɗa labarai da suka tabbatar da iƙirarin harbe-harbe ko hari a yankin a ranar da aka ambata.

Amurka ta tattare jami'anta a Abuja

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Amirka ta bukaci jami'anta da ke aiki a birnin tarayya Abuja su tattare kayansu su koma gida.

Ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar game da yanayin tsaro da ta ce ya samu koma baya a fadin Najeriya a yanzu.

Bugu da kari, Amurka ta bukaci 'yan kasarta su kiyayi zuwa wasu jihohi da suka hada da Filato, Benue, Taraba, Yobe, Borno, Bayelsa da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng