An Yi Rashi: Yadda 'Yan Ta'addan ISWAP Suka Kashe Babban Janar da Sojoji 17 a Borno
- 'Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun kai mummunan hari kan wani sansanin dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno
- Harin ya yi sanadiyyar mutuwar Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah, sojoji 17 da 'yan ta'adda da dama
- 'Yan ta'addan sun kuma kashe fararen hula tare da yin satar abinci a shaguna yayin kazamin harin da suka kai
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah da sojoji 17 ne suka rasa rayukansu yayin wani harin 'yan ta'addan ISWAP a Borno.
Sojojin sun rasu ne a hare-haren da ISWAP ta kai a sansanonin sojoji a Benisheikh ƙaramar hukumar Kaga, da Ngamdu, da kuma garin Pulka da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.

Source: Facebook
Majiyoyi daga cikin garin Benisheikh sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun yi ta harbin sansanin sojin ba kakkautawa, lamarin da ya janyo asarar rayuka masu yawa.

Kara karanta wannan
Rundunar sojoji ta tabbatar da kashe jami'anta, an ji abin da ta ce kan kisan Janar
'Yan ta'adda sun kashe Janar da sojoji
Marigayi Birgediya Janar Braimah shi ne Kwamandan Birged ta 29 (29 Task Force Brigade) mai hedikwata a Benisheikh.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta'addan bayan sun mamaye sansanonin sojoji guda uku da manyan makamai da bama-bamai, inda suka kashe aƙalla sojoji da jami’ai 18, har da Janar ɗin, tare da raunata wasu da dama dake cikin mawuyacin hali.
“Kwamandan birged ɗin, mataimakinsa, da limamin birged ɗin, gami da wasu jami’ai da sojoji da dama ne aka kashe a harin da aka kwashe sa’o’i ana fafatawa."
- Wata majiya
An kashe fararen hula
Sun bayyana cewa an kuma kashe fararen hula, sauran jami’an tsaro, da kuma ɗimbin ’yan ta’addan ISWAP yayin hare-haren tsakar daren da aka kai a lokaci guda.
A cewar majiyoyin, ’yan ta’addan sun afkawa garin Benisheikh da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilun 2026, inda suka ƙone manyan motocin ɗaukar kaya da motocin kasuwanci da dama.
Maharan sun kuma kashe direbobi da fasinjoji waɗanda suke kan tafiya suka tsaya don kwana a garin, saboda saba rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu da yamma.
'Yan ta'addan ISWAP sun yi barna
Wani mazaunin Benisheikh da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa:
“Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da dama a Benisheikh. Sai dai abin takaici, wasu jami’an tsaro ciki har da kwamandan birged ɗin sun rasa rayukansu, sannan ’yan ta’addan sun yi awon gaba da motoci da dama."

Source: Twitter
A cewar rahotanni, ’yan ta’addan sun kuma kwashe kayan abinci daga shaguna a garin Pulka, sannan suka lalata wasu ababen more rayuwa, ciki har da injina da kayan aikin wani kamfanin ginin hanya, Decency Associates, inda suka ƙone motocin da darajarsu ta kai ɗururuwan miliyoyin nairori.
Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe sojojin a shafinta na X, amma ba ta ce komai ba kan mutuwar Birgediya Janar Oseni Braimah.
Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin 'yan ta'addan Boko Haram a sansaninsu da ke Malam Fatori a jihar Borno.
Yan ta’addan, wadanda suka taso da yawa a kafa tare da amfani da jirage marasa matuka masu dauke da makamai domin kai hari sun gamu da turjiya mai karfi daga dakarun.
Dakarun sojojin sun samu nasarar fatattakar maharan tare da kashe akalla ‘yan ta’adda 80 a yayin fafatawar.
Asali: Legit.ng

