Lamari Ya Sauya: Ƴan Bindiga Sun Bukaci Daruruwan Shanu, Dabbobi a matsayin Haraji

Lamari Ya Sauya: Ƴan Bindiga Sun Bukaci Daruruwan Shanu, Dabbobi a matsayin Haraji

  • ’Yan bindiga sun bukaci daruruwan dabbobi a jihar Katsina a matsayin haraji ga wasu al'ummomi da ke yankin
  • Maharan sun ce dole a kawo shanu da tumaki daga wasu kauyuka yayin da suke barazanar kai hari idan ba a biya ba
  • Wannan bukata ta jefa mazauna cikin firgici, inda jama’a daga kauyuka da dama suka tsere, suka bar gidajensu domin tsira daga yiwuwar hare-hare

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kankia, Katsina - ’Yan bindiga sun bukaci wasu yan ƙauyuka a jihar Katsina da su biya haraji da dabbobi saboda gudun kai masu farmaki kamar yadda aka saba.

Maharan sun bukaci shanu 700 da tumaki 1,000 daga wasu kauyuka uku a karamar hukumar Kankia da ke Katsina, suna barazanar kai hari idan ba a biya ba.

Kara karanta wannan

Kujerar mataimakin Abba Kabir na neman jawo rigima, an roki Tinubu kan Sule Garo

Yan bindiga sun yi barazanar kai hari kan ƙauyukan Katsina
Taswirar jihar Katsina da ake fama da hare-haren yan ta'adda. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan bindiga sun addabi ƙauyukan Katsina

An isar da sakonnin bukatar ta hanyar wasiku zuwa kauyukan Rimaye da Sukunturi ranar 6 ga Afrilun 2026, inda aka bai wa mazauna wa’adin kwanaki hudu, cewar Daily Trust.

Wani mazaunin yankin, Malam Ahmadu Kankia, ya ce wannan wasika ta haddasa tsoro, inda jama’a daga Kunduru, Sukunturi, Tsa da Magam suka tsere daga gidajensu.

Ya ce:

“An kawo wasiku daban-daban amma duk suna dauke da bukata iri daya, mutane sun firgita sosai har suka fara gudu, yanzu kauyukan sun zama kufai.”
Mazauna yankunan Katsina sun koka kan harajin yan bindiga
Gwamna Dikko Umaru Radda yayin kaddamar da rundunar tsaro a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Da wane yare yan bindiga suka rubuta wasikun?

Wani mazaunin yankin, Usman Dada, ya ce an rubuta wasikun da Turanci, kuma al’umma sun yanke shawarar komawa wurare mafi aminci a cikin Kankia saboda tsoron hare-hare.

Rahotanni sun ce wasu mazaunan kan shiga kauyukansu da rana domin kwaso ragowar dabbobi, saboda hare-hare na faruwa ne da sassafe ko kuma da yamma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta jero jihohi 10 da za a yi ambaliyar ruwa

Wata majiyar al’umma ya ce sun kwaso dabbobinsu suka kai kasuwa domin sayarwa, inda ya kara da cewa babu wanda ke son komawa kauyukan a yanzu, cewar Sahara Reporters.

Hare-haren yan bindiga na jawo matsala a Katsina

Wannan lamari na zuwa ne yayin da hare-haren ’yan bindiga ke sake karuwa a jihar, bayan wani dan takaitaccen shirin zaman lafiya da aka cimma watanni da suka gabata.

Sababbin hare-haren sun janyo damuwa sosai, lamarin da ya sa gwamnatin Katsina ta kira taron gaggawa tare da jami’an tsaro domin daukar matakan shawo kan matsalar.

An cafke mata da ke taimakon yan bindiga

Mun ba ku rahoton cewa jami'an hukumar DSS sun kama wata mata mai shekaru 25 da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga harsasai a Kano.

An cafke ta da harsasai 200 da aka ce an kawo daga wata jiha, inda ta shirya safararsu ta Kano zuwa ga ƴan bindiga a Katsina da ke fama da matsalolin hare-haren yan ta'adda.

Ta amsa laifi tare da fallasa wasu da ake zargin suna da hannu a harkar, har da wanda ya ɗora ta a muguwar sana'ar yayin da ta yi nadama kan abubuwan da ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.