‘Ku Kwantar da Hankulanku’: Martanin Najeriya bayan Gargadin Amurka a Abuja

‘Ku Kwantar da Hankulanku’: Martanin Najeriya bayan Gargadin Amurka a Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta yi martani bayan Amurka ta bukaci wasu yan kasarta da su yi gaggawar barin Abuja
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana gargadin a matsayin matakin kariya na cikin gida ba matsalar tsaro ba
  • Gwamnati ta ce ana samun ci gaba a harkar tsaro ta hanyar ayyukan sojoji da bayanan sirri da ake samu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa kasar na nan cikin kwanciyar hankali kuma tana aiki yadda ya kamata.

Hakan ya biyo bayan wani gargadi da Amurka ta fitar inda ta bukaci wasu yan kasar da su fice daga birnin Abuja.

Najeriya ta magantu bayan gargadin Amurka
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Hakan na cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya fitar wanda ma'aikatar ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta jero jihohi 10 da za a yi ambaliyar ruwa

Najeriya ta magantu bayan gargadin Amurka a Abuja

A cikin sanarwar, Mohammed Idris ya ce dukkan cibiyoyin gwamnati na ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Sai dai gwamnati ta bayyana wannan mataki a matsayin na kariya kawai, bisa tsarin cikin gida na jakadanci, ba wai yana nuni da halin tsaro na kasa baki daya ba.

Ya kara da cewa babu wani cikas ga tafiyar da gwamnati, tattalin arziki, ko rayuwar yau da kullum a fadin kasar.

Ministan ya ce hukumomin tsaro na samun nasarori a ayyukansu ta hanyar hadin gwiwar sojoji, amfani da bayanan sirri, da kuma ingantaccen hadin kai tsakanin hukumomi.

A cewarsa, wadannan kokari sun taimaka wajen dakile ayyukan kungiyoyin masu laifi tare da inganta tsaro a yankuna daban-daban na kasar.

Ya ce:

“Hukumomin tsaro na ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyi, kuma ana ganin sakamakon wadannan kokari a zahiri.”
Najeriya ta tabbatar da ingancin tsaro a kasar
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi tagumi yayin taro a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Yadda Najeriya ta bude kofa ga kowa

Ministan ya kara da cewa Najeriya na bude ga kasuwanci, yawon bude ido da kuma zuba jari, inda gyare-gyaren tattalin arziki ke kara karfafa amincewar masu zuba jari.

Kara karanta wannan

Bayan hare haren da aka kai a jihohin Arewa, Tinubu ya tunkari matsalar tsaro gadan gadan

Ya bukaci kasashen duniya da abokan hulda su dogara da sahihan bayanai kuma sababbi game da halin tsaro a Najeriya.

Sanarwar ta biyo bayan gargadin tsaro da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar, wanda ya jawo hankalin jama’a da tattaunawar diflomasiyya.

Gwamnatin Najeriya ta jaddada cewa irin wadannan gargadi na kasashen waje ba su canza gaskiyar cewa ana samun ci gaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na kasar ba.

Najeriya ta magantu kan yakin Iran da Isra'ila

A wani labarin, an ji cewa ministan yada labarai na kasa, Mohammed Idris, ya ce Najeriya a shirye take ta taimaka wajen magance rikicin makamashi da ke faruwa a duniya.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi a rikicin Gabas ta Tsakiya, a wata hira da ya yi.

Kalaman Mohammed Idris sun fara janyo martani iri-iri daga ‘yan Najeriya, inda wasu suka koka cewa har yanzu kasar ba ta iya biyan bukatun cikin gida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.