'Yan Bindiga Saman Babura 50 Sun Yi Ta'asa a Zamfara, an Kashe Jami'an Tsaro
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka jami'an tsaro na 'yan sanda da fararen hula yayin harin da suka kai a wani kauye
- Jami'an 'yan sanda sun yi artabu da su, inda suka hallaka wasu daga cikinsu tare da raunata wasu da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda da fararen hula yayin wani hari da suka kai a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kashe mutane biyar, da suka haɗa da jami'an sanda biyu da fararen hula uku, yayin wani hari da suka kai a kauyen Yarkatsinan Laka da ke ƙaramar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Legit Hausa ta samu daga wajen kakakin rundunar 'yan sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, a ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026.
'Yan sanda sun yi gumurzu da 'yan bindiga
DSP Yazid Abubakar ya bayyana cewa ’yan bindigan, waɗanda suka zo kan babura fiye da 50 kuma ɗauke da manyan makamai, sun mamaye garin ne a ranar Talata, 7 ga watan Afirilun 2026.
Sanarwar ta ƙara da cewa sashen kar-ta-kwana na ’yan sanda ya mayar da martani cikin gaggawa inda suka fafata da maharan.
Ya bayyana cewa fafatawar ta kai ga kashe ’yan bindiga 11 yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Sai dai kuma, sanarwar ta nuna cewa jami’an sanda biyu da fararen hula uku sun rasa rayukansu a lokacin fafatawar.
“Abin takaici, yayin musayar wuta, jami’an sanda biyu da fararen hula uku sun rasa rayukansu. Jami’in sanda ɗaya kuma ya samu rauni kuma a halin yanzu yana karɓar magani inda yake samun sauƙi."
- DSP Yazid Abubakar
Kwamishinan 'yan sanda ya je ta'aziyya
A cewar DSP Yazid, an riga an mayar da doka da oda a yankin tun bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan
An ga tashin hankali da 'yan bindiga suka farmaki tawagar babban kwamandan sojoji

Source: Twitter
Bayan harin, kwamishinan ’yan sandan jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Bello, ya kai ziyarar ta’aziyya ga mutanen garin Yarkatsinan Laka domin jajantawa iyalai da suka rasa rayukansu da kuma daukacin al’ummar garin kan wannan mummunan lamari.
Ya sake tabbatar wa mazauna yankin ƙudirin rundunar na ƙarfafa tsaro da kuma maido da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba wa jami’an tsaro haɗin kai tare da ba su sahihan bayanai akan lokaci domin inganta ayyukan tsaro.
'Yan bindiga sun farmaki kwamandan sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan tawagar kwamandan 'Sector 2' na rundunar Operation Fansan Yamma, a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Dakarun sojoji da ke cikin tawagae sun kashe ’yan bindiga da dama yayin fafatawar da aka yi sakamakon kawo harin.
A cewar majiyoyi soja ɗaya ne ya riga mu gidan gaskiya a lokacin gumurzun da aka yi da 'yan bindigan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
