An Fitar da Bidiyon Shugaban APC Yana Rawa a Kano, Abba Kabir Yana Masa Tafi
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya tika rawa a jihar Kano yayin da ya kai ziyarar aiki a makon da muke ciki
- Bidiyon rawar da ya yi ya dauki hankalin 'yan Najeriya, musamma yadda aka kalli gwamna Abba Kabir Yusuf yana masa tafi a wajen
- 'Yan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon, wasu na cewa ya yi daidai, wasu kuma na sukar shi da jam'iyyar APC
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya dauki hankalin al'umma yayin da ya yi rawan wakar Omologo a jihar Kano.
Mawakin da ya ke yi wa shugabannin APC waka, Dauda Kahutu Rarara ne ya yi wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wakar a shekarar 2025.

Source: Facebook
Shafin jam'iyya mai mulki na APC New New Media ne ya wallafa bidiyon yadda Yilwatda ya yi rawa a gaban gwamna Abba Kabir Yusuf a kafar X.
Shugaban APC ya yi rawa a gaban Abba
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana a wani bidiyo da ya yadu yana rawa da wakar Shugaba Bola Ahmed Tinubu mai taken “Omologo” yayin wata ziyara da ya kai Kano.
Bidiyon ya nuna Yilwatda yana waka da rawa tare da magoya bayan jam’iyyar a wani taron da ya samu halartar gwamna Abba KAbir Yusuf.
An hango gwamnan Kano yana yi wa shugaban APC tafi a wajen da ya ke rawan, yayin da wasu jama'a da dama suka rika rawa tare da Farfesa Nentawe Yilwatda.
Ga bidiyon rawan da Nentawe Yilwatda ya yi:
Ra’ayoyin ‘yan Najeriya kan bidiyon
'Yan Najeriya da dama sun nuna damuwa game da rawan da shugaban ya yi lura da halin da kasar ke ciki, yayin da wasu suka yaba masa.
SnatchTheBag ya ce:
"Wannan abin takaici ne. Shugabannin da suka yi alkawarin gyara wadannan matsaloli yanzu sun koma rawa tare da kama-karya maimakon yin aikin da aka zabe su su yi. Najeriya, yaushe za ki cigaba?
Bayan ganin Abba Kabir Yusuf da jar hula, Naomi ta tambaya:
"Me yasa aka cika wurin da hulunan Kwankwasiyya?
Machief Ayuba Mallo ya ce:
"Shugaba mai cikakken iko. Aikinka na kyau, ranka ya dade."

Source: Facebook
Muhammad ya ce:
"Mutane na cikin yunwa, wasu na mutuwa saboda babu tsaro, amma ku kuna rawa."
Deevine ya ce:
"Wannan jam’iyya ce maras hankali. Ku ji dadin ku a yanzu, domin nan gaba kadan ba ku ba ne."
Mohammad Amin Kabir Bayero ya ce:
"Duk lokacin da suka zo Kano, rawa kawai suke yi saboda babu abin da za su yi na kirki."
Chukwunonso ya ce:
"Ku yi rawa yau, gobe za ku yi kuka."
'Dan sarkin Daura ya shiga siyasa
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan Mai martaba Sarkin Daura, Muhammad Daha Umar Faruk ya sanar da cewa ya shiga siyasa.
Daha ya bayyana cewa bayan matsin lamba daga jama'a, ya amince ya yi takara domin neman kujerar majalisar wakilai a zaben 2027.
Duk da ya tabbatar da cewa ya shiga siyasa, Muhammad Daha bai fadi a jam'iyyar da zai yi takara ba, amma wasu sun ce zai iya shiga APC ko ADC.
Asali: Legit.ng


