Matatar Dangote Ta Yi Babban Rangwame, Ta Sauya Farashin Litar Fetur a Najeriya
- A yammacin ranar Laraba, matatar man Dangote ta janye ƙarin ₦75 da ta yi a kan farashin da take sayar wa 'yan kasuwa litar fetur
- Faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, sakamakon tsagaita wutar Amurka da Iran, shi ne babban dalilin wannan rangwame
- Farashin ɗanyen man Brent ya sauka zuwa $94.76, yayin da man WTI ya ragu zuwa $97.88, lamarin da ya sa Dangote sauke farashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas – A wani mataki na ba-zata da zai kawo sauƙi ga ƴan Najeriya, matatar man Dangote ta sanar da janye ƙarin farashin man fetur da ta yi a baya.
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa matatar man Dangote ta sauya farashin litar fetur zuwa ₦1,275 daga ₦1,200 a daren ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan
Yaƙi bai ƙare ba: Iran ta ƙaddamar da sababbin hare hare kan Saudiyya da ƙasashe 3

Source: UGC
Matatar Dangote ta sauke farashin fetur
Amma a wani rahoto da jaridar Punch ta fitar, an ji cewa matatar man ta janye wannan kari da ta yi, inda ta maida farashin kowace litar zuwa zuwa ₦1,200.
Wannan mataki ya biyo bayan gagarumar faɗuwar farashin ɗanyen mai da aka samu a kasuwar duniya sakamakon tsagaita wutar Iran da Amurka a yakin Gabas ta Tsakiya.
Idan ba a manta ba, a daren Talata, Dangote ya ce ya ƙara farashin zuwa ₦1,275 ne saboda tsadar danyen mai da yaƙin ya jawo, amma saurin faduwar danyen mai saboda tsagaita wutar ya tilasta janye wannan ƙarin yau.
Jami'an matatar sun tabbatar da cewa yanzu farashin da ake kai wa 'yan kasuwa ya koma ₦1,200, yayin da farashin da ake sayarwa a gaɓar teku ya tsaya a kan ₦1,153.
'Yan Najeriya za su samu sauki
A cikin wata sanarwa da matatar ta fitar, ta jaddada cewa babu wani sabon ƙarin farashi da ta aiwatar, kuma suna ƙoƙarin tabbatar da cewa kwastomominsu sun samu mai a kan farashi mai sauƙi.

Kara karanta wannan
Amurka da Iran na tsagaita wuta, matatar Dangote ta sauya farashin fetur a Najeriya
Wani babban jami’in matatar Dangote ya tabbatar da cewa:
"Eh, an janye ƙarin farashin; wannan ya biyo bayan saukar da aka samu na farashin ɗanyen mai a duniya yau."
Masana tattalin arziki na ganin cewa wannan mataki na Dangote zai taimaka wajen dakile tashin farashin kayayyaki da sufuri a Najeriya.

Source: Getty Images
Tasirin tsagaita wuta ga farashin mai
Babban dalilin wannan sauyin farashi shi ne sanarwar tsagaita wutar makonni biyu da Shugaba Donald Trump ya yi da ƙasar Iran.
Wannan labari ya kore fargabar cewa za a samu cikas wajen samar da mai daga Gabas ta Tsakiya, wanda hakan ya janyo farashin ɗanyen man Brent ya faɗi da kashi 13.28 zuwa $94.76 a kowace ganga.
Haka kuma, man Amurka na West Texas Intermediate (WTI) shi ma ya ragu da kashi 14.72 zuwa $97.88, kamar yadda rahoton Economic Times ya nuna.
'Yan kasuwa sun sauya farashin fetur
Tun da fari, mun ruwaito cewa, dillalan man fetur ta Najeriya (MEMAN) ta sanar da cewa kuɗin shigo da litar fetur ya haura N1,380 a farkon watan Afrilu.
A cewar MEMAN, farashin gangar ɗanyen mai na Brent ya kai kusan $108, yayin da Bonny Light na Najeriya ya haura $100, wanda hakan ya jawo tsadar fetur.
MEMAN ta fitar da rahoton yadda ake sayar da fetur, dizal, gas din girki, gas din CNG, man jirgi a wasu sassan Najeriya kamar Legas da Warri.
Asali: Legit.ng
