An Yi Babban Rashi a Najeriya, Mahaifiyar Mataimakin Gwamna Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Babban Rashi a Najeriya, Mahaifiyar Mataimakin Gwamna Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Edo, Madam Esther Imaguomwanruo ta rasu tana da shekaru 95 a duniya
  • Iyalan marigayiyar sun tabbatar da cewa ta mutu ne a safiyar yau Laraba, 8 ga watan Afrilu, 2026 bayan fama da rashin lafiya
  • Sun bayyana Madam Esther a matsayin uwa mai daraja, wacce ta kasance abin koyi ta fuskar imani, kwarjin hali, da sadaukarwa ga iyalanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - An shiga jimami da alhini a jihar Edo da ke Kudancin Najeriya bayan samun labarin rasuwar mahaifiyar mataimakin gwamna, Hon. Dennis Idahosa.

An tabbatar da rasuwar Madam Esther Imaguomwanruo, mahaifiyar mataimakin gwamnan Jihar Edo, Dennis Idahosa, ne a yau Laraba, 8 ga watan Afrilun 2026.

Idahosa.
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Hon. Dennis Idahosa da marigayiya Madam Esther Imaguomwanruo Idahosa Hoto: Hon. Dennis Idahosa
Source: Facebook

Mataimakin gwamnan jihar Edo ya yi rashi

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Madam Esther ta rasu ne a Benin City, babban birnin jihar Edo da safiyar ranar 8 ga Afrilu, 2026, bayan gajeriyar jinya tana da shekaru 95 a duniya.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala: Abubuwan da ya kamata a sani game da matashin da ke neman hana ruwa gudu a ADC

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Friday Aghedo, ne ya tabbatar da rasuwarta a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin Dennis Idahosa na Facebook, iyalan Enabulele na karamar hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma a Jihar Edo sun bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

Iyalan marigayiya sun fitar da sanarwa

Sun kuma bayyana cewa marigayiyar ta rasu cikin kwanciyar hankali a cikin iyalanta tare da bayyana cewa za su yi kewarta saboda yadda ta zame masu uwa.

Sanarwar ta ce:

“Iyalin Enabulele na sanar da rasuwar ‘yarsu, uwa kuma kaka, Madam Esther Imaguomwanruo Idahosa, wadda ta rasu cikin kwanciyar hankali ranar Laraba, 8 ga Afrilu, 2026, tana da shekaru 95.”
Mama Idahosa, mahaifiyar Hon. Dennis Idahosa, Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, mace ce mai daraja wacce ta rayu tsawon rai, cike da nasarori da kuma ayyukan kwarai.
"Rayuwarta ta kasance abin koyi ta fuskar imani, kwarjin hali, da sadaukarwa ga iyalanta da ma al'umma baki daya. Kyawawan dabi'unta na hikima sun kasance abin alfahari da kwarin gwiwa ga duk wanda ya san ta."

Kara karanta wannan

Bayan ya yi murabus, Majalisa ta canza shawara kan mataimakin gwamnan jihar Kano

Dennis Idahosa.
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Hon. Dennis Idahosa Hoto: Hon. Dennis Idahosa
Source: Facebook

Za a sanar da lokacin jana'izarta

A cewarsu, ta shafe shekaru da dama tana taka muhimmiyar rawa wajen tarbiyyar ‘ya’ya da jikoki, gina kyakkyawan alaka a cikin al’umma da kokarin inganta rayuwar jama’a ta hanyar nasiha da goyon baya

Ta kuma kasance mace mai tsananin imani, wadda ta sadaukar da rayuwarta ga bautar Allah da kuma hidimar iyali da al’umma.

A karshe, sanarwar ta yi addu'ar samun salama ga Madam Esther Imaguomwanruo, sannan ta ce za a sanar da shirye-shirye jana'iza nam ba da jimawa ba.

Hadimin gwamnan Delta ya rasu a taro

A wani rahoton, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar babban mai tsara ayyukan Gwamnan jihar Delta, Sunday Kotor bayan ya yanke jiki ya fadi a wurin taro.

Gwamnan jihar Delta, Sheriff Ooborevwori, ya nuna matukar alhini kan rasuwar Mai Taimaka Masa na Musamman kan harkokin tsare-tsare, Sunday Kotor.

Gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, musamman kaninsa Conference Kotor, wanda shi ma ke aiki a matsayin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262