Amurka da Iran na Tsagaita Wuta, Matatar Dangote Ta Sauya Farashin Fetur a Najeriya

Amurka da Iran na Tsagaita Wuta, Matatar Dangote Ta Sauya Farashin Fetur a Najeriya

  • Matatar man Dangote ta ƙara ₦75 kan litar fetur da take sayar wa 'yan kasuwa, wanda ya mayar da farashin zuwa ₦1,275 yanzu
  • Shi ma farashin dizil ya yi tashi, inda aka samu ƙarin ₦200, wanda a yanzu lita ɗaya ta kama ₦1,950, kuma ake fargabar zai kai ₦2,000
  • Duk da rahotannin saukar farashin man Brent a bayan tsagaita wutar Amurka da Iran, matatar Dangote ta danganta ƙarin da rikicin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas – A daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki, matatar man Dangote ta ƙara farashin man fetur da dizil a daren jiya Talata, 7 ga Afrilu, 2026.

Wannan matakin ya ƙara jefa fargaba ga masu sana'o'i, kamfanoni, da ma duk wanda yake dogara da mai don ayyukansu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

Matar Dangote ta kara kudin litar man fetur a Najeriya
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da wani mutumi yana sayar da mai. Hoto: Bloomberg via Getty Images
Source: Getty Images

Matatar Dangote ta kara kudin man fetur

Wani babban jami’in matatar wanda ya tabbatar da wannan labari ya bayyana cewa an sauya farashin fetur din ne domin dacewa da yanayin kasuwar duniya, in ji rahoton Punch.

A cewarsa, matsin lamba da ake fuskanta a yankin Gabas ta Tsakiya ya janyo tashin farashin ɗanyen mai a duniya, wanda hakan kuma dole ne ya shafi farashin tataccen mai.

Sabon tsarin farashin ya nuna cewa litar fetur ta tashi daga ₦1,200 zuwa ₦1,275, wanda ke nuna ƙarin kashi 5.02 cikin 100.

Dizil zai kara tsada a gidajen mai

Mafi girma shi ne farashin dizil wanda ya yi tsalle daga ₦1,750 zuwa ₦1,950, ƙarin ₦200 ke nan a kowace lita daga yadda ake sayar da shi a baya.

Wannan na nuna cewa nan ba da jimawa ba dizil zai iya haura ₦2,000 a gidajen mai, lamarin da zai iya janyo tsadar sufuri da kayan abinci.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da sanarwa da Amurka ta yarda ta tsagaita wuta da kasar Musulunci

Legit Hausa tana da labari cewa farashin kowane lita na dizil ya doshi N2, 000 a gidajen mai dake Kaduna.

Rikicin Gabas ta Tsakiya ya shafi Najeriya

Haka kuma, bayanan da aka samu daga shafukan lura da farashin man fetur sun tabbatar da cewa wannan ƙarin ya fara aiki tun a matakin dauko fetur din daga matatar, in ji rahoton Leadership.

Duk da fatan da ake da shi na cewa tace mai a cikin gida zai kawo sauƙin farashi, masana tattalin arziki sun bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin tasirin kasuwar duniya.

Muddin dai ɗanyen mai ya ci gaba da tashi a duniya, farashin fetur a gida ba zai tsaya wuri ɗaya ba domin matatun man ma a kan farashin duniya suke sayen ɗanyen man.

A halin yanzu, ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana damuwarsu kan yadda wannan ƙarin zai shafi rayuwarsu.

Masana na fargabar idan aka ci gaba da tafiya a haka, farashin fetur zai haura N2,000.
Wani ma'aikaci yana sayar fetur a gidan mai. Hoto: Benson Ibeabuchi/Bloomberg via Getty Images
Source: Getty Images

Tsagaita wuta ya sauke farashin mai

Amma a hannu daya, rahoton Sky News ya nuna cewa, farashin danyen mai ya sauka kasa a kasuwar duniya, yayin da aka samu tashin farashi a kasuwar hannayen jari bayan Amurka da Iran sun tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Ya haura N1,215: Ƴan kasuwa sun sanar da sabon farashin man fetur a Najeriya

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa, farashin danyen man Brent ya sauka da kusan kashi 14, inda ganga daya ta koma $94 daga $100.

'Yan kasuwa sun sauya farashin fetur

Tun da fari, mun ruwaito cewa, dillalan man fetur ta Najeriya (MEMAN) ta sanar da cewa kuɗin shigo da litar fetur ya haura N1,380 a farkon watan Afrilu.

Farashin gangar ɗanyen mai na Brent ya kai kusan $108, yayin da Bonny Light na Najeriya ya haura $100, wanda hakan ya jawo tsadar tataccen mai.

MEMAN ta fitar da rahoton yadda ake sayar da fetur, dizal, gas din girki, gas din CNG, man jirgi a wasu sassan Najeriya kamar Legas da Warri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com