An Gurfanar da Mutane 20 da Ake Zargi da Hannu a Ayyukan Ta'addanci a Najeriya

An Gurfanar da Mutane 20 da Ake Zargi da Hannu a Ayyukan Ta'addanci a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dawo da shari'o'in wadanda ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci a Najeriya
  • An gurfanar da mutane 20 a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja yau Talata, lamarin da ke nuna sauyi a shari'o'in 'yan ta'addan
  • Bayanai sun nuna cewa an girke jami'an tsaro a muhimman wurare da titunan zuwa kotun domin tabbatar da tsaro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da shari’ar dinbin mutanen da ake zargi da hannu a ayyyukan ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Rahoto ya nuna cewa gwamnatin ta gurfanar da akalla mutane 20 a gaban babbar kotun mai zama a Abuja yau Talata, 7 ga watan Afrilun 2026.

Kotun tarayya.
Harabar babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An maida shari'o'in yan ta'adda Abuja

Kara karanta wannan

An kama mai suna 'John' cikin masu kai hari a kungiyar Boko Haram

Jaridar Leadership ta rahoto cewa hakan ke nuna wani gagarumin sauyi daga yadda aka saba gudanar da shari’o’in 'yan ta'addan a wuri guda a Kainji, jihar Neja.

Shari’ar, wadda ta shafi wadanda ake zargi visa tuhume-tuhume da suka shafi ta’addanci, an mayar da ita Abuja ne a lokacin da kotun bikin Easter.

A cewar rahotanni, hutun wanda aka fara ranar 7 ga watan Afrilu, zai kare ne a ranar 13 ga watan Afrilu, inda ake sa ran za a ci gaba da zaman kotu a dukkan shiyyoyi a ranar 14 ga watan Afrilu, 2026.

Duk da ana tsakiyar hutu hutun, an ware akalla dakunan shari’a 13 a reshen Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin tunkarar tarin shari’o’in ta’addancin, lamarin da ke nuna girman aikin da kuma bukatar gaggawa wajen gudanar da shari’o’in.

Tawagar lauyoyin gwawmnatin Najeriya tana karkashin jagorancin Darakta Janar na Hukumar Bada Agajin Shari’a ta Tarayya, Aliyu Abubakar.

Sunayen wadanda aka gurfanar a kotu

Aliyu ya bayyana a gaban Mai Shari’a Binta Nyako tare da sauran lauyoyi domin gurfanar da wasu mutane kusan 20 da ake zargi da hannu a ayyaukan ta'addanci.

Kara karanta wannan

Wuya ta yi wuya: Isra'ila ta dakatar da kai hare hare kan kasar Iran, an ji dalili

Wadanda sunayensu suka fito a jadawalin shari’ar kotun sun hada da Hamat Modu, Isah Ali, Awal Bello, Shehu Bukar, Alhaji Kulle, Mohammed Abacha Hassan, Aminami Mallum, Tasiu Yakubu, da Abdullahi Ali, da dai sauransu.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman kotu Hoto: Joe Raedle
Source: Getty Images

An girke jami'an tsaro a Abuja

An tsaurara matakan tsaro sosai a kewayen kotun, inda aka girke karin dakarun tsaro dauke da makamai zuwa wurare daban-daban, cewar rahoton Vanguard.

An katange dukkan hanyoyin da ke kaiwa zuwa Babbar Kotun Tarayya, yayin da jirage masu saukar ungulu na ‘yan sanda suka ci gaba da shawagi a sararin samaniyar yankin kasuwanci na tsakiyar birnin (CBD) da ke Abuja.

An gurfanar da makasan Fatima a kotu

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun jihar Kano ta fara zaman sauraron shari'ar wadanda ake zargi da kisan Fatima da 'ya'yanta shida a unguwar Dorayi.

Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da wadanda ake zargi su hudu ciki har da dan uwan marigayiyarsa mai suna Umar, a gaban Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Bompai.

Yayin zaman kotun, mutane uku daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifuffukan da da aka bayyana, sun ki amsa laifi yayin da wanda ake kara na farko, Umar Auwalu, ya amsa laifinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262