Ba zai Ga 2027 ba: Babban Dan Siyasa Kuma Shugaban Majalisar Kebbi Ya Rasu
- Rahotanni sun nuna cewa an tabbatar da rasuwar shugaban majalisar dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru a kasar waje
- Shugaban ya rasu ne a wani asibiti a kasar Masar bayan jinya kan wata cuta da ba a bayyana ga manema labarai ba har zuwa yanzu
- Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Kebbi da kasa baki daya yayin da ta tabbatar da cewa sauran bayanai na tafe
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - An shiga jimami a Jihar Kebbi bayan sanar da rasuwar Shugaban majalisar dokokin jihar, Muhammad Usman Zuru, wanda ya rasu a daren Litinin.
Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke kasar Masar inda yake karbar magani kan wata cuta da ba a bayyana ba.

Kara karanta wannan
Matasa sun dauki mataki mai muni da aka kashe wani bawan Allah kan 'pure water' a Katsina

Source: Twitter
Tashar talabijin mallakar gwanatin Najeriya ta NTA ta tabbatar da rasuwar shugaban majalisar a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.
Shugaban majalisar jihar Kebbi ya rasu
Majiyoyi na kusa da gwamnatin jihar ne suka tabbatar da rasuwar Muhammad Usman Zuru, yayin da ake ci gaba da tattara karin bayani kan halin da ya shiga kafin mutuwarsa.
Kafin rasuwarsa, Muhammad Usman Zuru yana karbar magani ne a wani asibiti a kasar Masar, inda aka ce yana fama da wata cuta.
Har zuwa lokacin da ya rasu, babu cikakken bayani daga hukumomi kan irin rashin lafiyar da yake fama da ita. Wannan ya sa mutane da dama ke jiran karin bayani daga gwamnati ko makusantansa.
Rawar da ya taka a majalisar Kebbi
Punch ta wallafa cewa Marigayin ya kasance wakilin mazabar Zuru a majalisar dokokin Jihar Kebbi, kuma ana kallonsa a matsayin daya daga cikin jiga-jigan majalisar.
A matsayinsa na Shugaban majalisa, ya taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin dokoki da kuma jagorantar ayyukan majalisar kafin rasuwarsa.

Source: Original
Bayanin gwamnatin jihar Kebbi
Wani hadimi ga gwamnan jihar kan harkokin sadarwa, Idris Zuru, ya tabbatar da rasuwar tare da bayyana ta a matsayin abin da ya girgiza su.
Ya ce:
“Rasuwar shugaban majalisar, Rt. Hon. Muhammad Usman Zuru, ta zo mana a matsayin babban tashin hankali. Wannan babban rashi ne ba ga Jihar Kebbi kadai ba har ma da kasa baki daya.”
Ya kara da cewa gwamnati na ci gaba da tattara cikakkun bayanai kan rasuwar, kuma za ta fitar da sanarwa a hukumance tare da bayyana shirye-shiryen jana’iza bayan tuntubar iyalansa.
Ana sa ran gwamnati da iyalan marigayin za su sanar da karin bayani kan yadda za a gudanar da jana’izarsa nan gaba kadan.
Malamin Musulunci ya rasu a Bauchi
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi magana kan rasuwar Sheikh Isa Muhammad Bauchi.
Sheikh Bala Lau ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga al'ummar Bauchi, Najeriya da duniyar Musulunci baki daya.
Ya kuma yi addu'ar Allah ya gafartawa malamin tare da cewa an riga an masa sallar jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

