Yakin Iran: An Shiga Matsala a Najeriya, Farashin Magunguna Ya Karu da Kashi 30

Yakin Iran: An Shiga Matsala a Najeriya, Farashin Magunguna Ya Karu da Kashi 30

  • Rikicin Gabas ta Tsakiya na kara tasiri a Najeriya yayin da bangarorin rayuwa da dama ke ci gaba da sauyawa
  • Farashin kayan hada magunguna ya tashi da kusan 28% yayin da farashin man fetur ke kara haurawa a Najeriya
  • Masana sun yi gargadin yiwuwar karancin magunguna, lamarin da ka iya jefa majinyata cikin yanayi mai ban tsoro

Yayin da rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba ta’azzara, tasirinsa ya fara bayyana a sassa daban-daban na duniya, musamman a Najeriya.

Baya ga fannin man fetur da ‘yan kasar ke ci gaba da kuka kan tsadarsa, fannin hada magunguna na fuskantar matsin lamba mai tsanani.

Rahotanni sun nuna cewa matsalar katse hanyoyin kasuwanci na duniya da hauhawar farashin makamashi sun fara janyo karancin magunguna da tashin farashinsu, lamarin da ka iya haifar da babbar matsala ga lafiyar jama’a.

Yadda yakin Iran ya shafi Najeriya ta fannin magani
Magani ya tashi saboda yakin Iran Hoto: Mohammed Hamoud
Source: Getty Images

Dogaro da kayayyakin waje

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta jaddada cewa kasar na dogaro sosai da magungunan da ake shigowa da su daga kasashen waje, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Bana ka taba: Faransa ta tura sojoji da tankokin yaki domin a yaki Isra'ila

Ta yi nuni da cewa, ana shigo da yawan kayan ne daga yankin Asia, wanda ke sanya Najeriya cikin hadari idan aka samu tangarda a harkokin sufuri na duniya.

Babban abin damuwa shi ne yadda masana’antar magunguna ke amfani da kayan hada magani da ake shigo da su daga kasashe kamar India da China.

Duk wani tangarda a wadannan hanyoyi na kasuwanci na duniya na sa farashin magunguna ya tashi cikin gaggawa.

Farashin kayayyaki ya tashi

Shugaban kamfanin May & Baker Nigeria Plc, Patrick Ajah, ya bayyana cewa rikicin ya fara tasiri kai tsaye, inda aka soke wasu oda, yayin da farashin kayan hada magani kamar paracetamol ya karu da kusan 28%.

Ya kuma kara da cewa jinkirin jigilar kayayyaki da rashin samuwarsu cikin sauki na kara dagula al’amura.

Ko da yake Najeriya ba ta shigo da magunguna kai tsaye daga Gabas ta Tsakiya, katsewar manyan hanyoyin jiragen ruwa kamar mashigar Hormuz na da tasiri sosai, domin yawancin jigilar kaya a duniya na bi ta wannan hanya.

Rikicin ya kuma janyo hauhawar farashin mai da makamashi a duniya, wanda hakan ya kara tsadar samar da kayayyaki da jigilar su.

Kara karanta wannan

Yau ce ranar karshe: Abin da ya kamata ku sani kan cika bayanan haraji a Najeriya

Najeriya na dogaro da kayan magungunan waje
Yadda yakin Iran ya daga farashin magani a Najeriya | Hoto: GettyImages
Source: Getty Images

An bayyana cewa farashin dizal ya tashi sosai, lamarin da ke kara wa masana’antu nauyi.

Masana sun yi gargadin cewa kamfanoni ba za su iya ci gaba da daukar wannan karin farashi ba, dole ne su mayar da shi ga masu saye.

Karancin magunguna na iya tasowa

Masana sun ce idan lamarin ya ci gaba, ba wai farashin magunguna kawai zai tashi ba, har ma ana iya fuskantar karancinsu a kasuwa.

Shugaban kungiyar masu kantin magani ta Najeriya ya tabbatar da cewa farashin wasu magunguna, musamman wadanda ake shigowa da su daga waje, ya karu da kusan 30%.

Masana sun kuma yi gargadin cewa idan aka samu karancin magunguna, hakan na iya bude kofa ga yawaitar jabun magungunan, wanda zai kara jefa rayukan jama’a cikin hadari.

Bukatar gyara tsarin cikin gida

Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnati da ta zuba jari a cikin gida wajen samar da kayan hada magunguna domin rage dogaro da kasashen waje.

Kara karanta wannan

Pakistan ta faɗi halin da ake ciki a kokarin sulhunta Iran da Amurka

Sun ce idan aka ci gaba da wannan dogaro, duk wani rikici a duniya zai rika shafar lafiyar jama’ar Najeriya kai tsaye.

A cewar masana, akwai bukatar daukar matakai cikin gaggawa domin kare fannin lafiya daga irin wadannan matsaloli, domin idan aka bari, al’umma ce za ta fi shan wahala.

A karshe, sun gargadi cewa idan rikicin ya dauki lokaci mai tsawo, matsalar na iya tsananta, inda ko da mutum yana da kudi, zai iya rasa samun magunguna a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng