Zamfara: Yan Bindiga Sun Kakaba wa Kauyuka Harajin N16m, Sun Ba da Wa’adin Kwanaki

Zamfara: Yan Bindiga Sun Kakaba wa Kauyuka Harajin N16m, Sun Ba da Wa’adin Kwanaki

  • ‘Yan bindiga sun ba wasu mazauna kauyukan jihar Zamfara harajin miliyoyi inda suka yi masu barazanar kai hare-hare
  • Maharan sun kakabawa kauyuka uku a Zamfara harajin N16m tare da wa’adin kwanaki shida da barazanar hare-hare
  • An ce wani jagora mai suna Sojan Zakui ne ke jagorantar wannan umarni inda mazauna yankin ke cikin fargaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kakabawa kauyuka uku a karamar hukumar Bungudu ta Zamfara harajin miliyoyi.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun kakabawa kauyukan uku kudi har Naira miliyan shida ajihar da ke Arewa maso Yamma.

Yan bindiga sun kakaba wa yan Zamfara haraji
Taswirar jihar Zamfara da ke fama da matsalolin yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Zagazola Makama ya bayyana cewa kauyukan da abin ya shafa sun hada da Gidan Saro, Maje da Fanda Haki da ke yankin Kekun Waje.

Kara karanta wannan

An gano jam'iyyu 2 da Atiku, Kwankwaso za su iya komawa saboda tsaro kafin 2027

Zamfara: Yan bindiga sun hana manoma sakat

Wannan ba shi ne karon farko da mahara ke kakaba wa mazauna yankuna a Arewacin Najeriya haraji ba na makudan kudi.

Yayin da ake kokarin kwashe amfanin gona a yankunan karkara a shekarar da ta gabata, yan bindiga sun sake dawowa domin karbar kudi.

An tabbatar da cewa mutanen ƙauyuka a karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, sun ce ’yan bindiga suna tilasta musu biyan kuɗin “girbi”.

Maharan sun ce dole ne sai sun biya makudan kudi na miliyoyi kafin su shiga gonakinsu, duk da wahalar da ake ciki na rashin kudi.

Yan bindiga sun addabi al'ummar Zamfara
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Yadda yan bindiga suka kakaba haraji a Zamfara

An ce gungun ‘yan bindigar karkashin jagorancin wani da ake zargi mai suna Sojan Zakui ta sanar da wannan haraji tun ranar 31 ga watan Maris.

Sun kuma yi gargadin cewa duk wanda ya gaza biyan kudin zai fuskanci mummunan hari daga gare su.

Bayanai sun nuna cewa an bukaci Gidan Saro ya biya N5m, Maje N6m, yayin da Fanda Haki za ta biya N5m.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Na kusa da Gwamna Dauda Lawal ya sha da ƙyar a harin ƴan bindiga

Wannan ya kai jimillar kudin da ake nema zuwa N16m daga wadannan kauyuka uku wanda ya tayar da hankulan mazauna yankunan.

Haka kuma an ce ‘yan bindigar sun aika sakonni ta hannun wani da ake kira Hamidu domin jaddada barazanar.

Sun umarci mazauna yankin da su biya kudin cikin kwanaki shida ko su fuskanci hare-hare masu tsanani a yankin.

Rahotanni sun ce al’ummar yankin sun shiga tsananin fargaba sakamakon wannan barazana wanda ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Wasu daga cikin mazauna yankin na shirin barin gidajensu domin gujewa yiwuwar farmaki daga ‘yan bindigar.

Yan bindiga sun kakaba wa manoma haraji

A baya, mun ba ku labarin cewa al’ummar Bazar a Yabo ta jihar Sokoto sun roƙi gwamnatin jihar ta taimaka musu wajen biyan harajin da ‘yan bindiga suka kakaba musu.

Mutanen yankin sun bayyana cewa rashin biyan harajin na iya janyo kai musu hari da kuma lalata amfanin gonarsu da ya kammala nuna.

Wani mazaunin yankin, Alhaji Dauda Umar, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki sun sace mutane bakwai tare da sace kayayyaki masu daraja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.