Ana tsakiyar Bikin Kiristoci, Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane a Jihar Filato
- Ƴan bindiga sun yi wa matasa kwanton-ɓauna a Jos ta Kudu, inda suka buɗe musu wuta tare da kashe mutum uku
- Abin ya faru ne sa'ilin da matasan ke dawowa daga wurin hakar ma'adinai bayan sun kammala bikin Good Friday
- Shugabannin al'umma sun nuna damuwa kan yadda mahara ke mamaye dazuzzukan jihar, inda suka yi kira ga jami'an tsaro
Filato – Jihar Filato ta sake shiga cikin wani babban hali na jimami da fargaba a yau Asabar, 4 ga Afrilu, 2026, bayan kisan wasu matasa.
Wasu miyagun mahara sun buɗe wa matasan wuta, inda suka kashe mutum uku tare da raunata ɗaya a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.

Source: Original
Ƴan bindiga sun kashe matasa a Jos
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na daren jiya Juma'a a yankin Nyamgo Gyel cewar rahoton Punch.
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun fito ne daga wani wurin hakar ma'adinai dake Gero a daidai lokacin da maharan suka tare su.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa matasan waɗanda yawansu ya kai kusan 15 suna kan babura ne lokacin da maharan suka buɗe wuta.
Abin takaici, mutum uku ba su samu nasarar tserewa yayin da ake harbin ba, sannan ɗaya daga cikin su ya ji raunuka sosai.
Waɗanda aka kashe sun haɗa da Luka Pam, Samuel Davou da Deme Saidu, waɗanda duka matasa ne.
Bikin Good Friday ya koma makoki
Shugaban ƙungiyar matasan Berom (BYM), Solomon Dalyop, ya bayyana cewa matasan sun fita ne domin yin bikin ranar Good Friday kafin harin ya faru.
Dalyop ya bayyana cewa wannan kisa ya daga hankulan jama'a, musamman ganin yadda harin ya faru ana farin cikin bikin Kirista, in ji rahoton Premium Times.
Dung Davou, wani shugaban matasa a yankin Gyel, ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin dakatar da waɗannan hare-haren dake yawan faruwa a cikin garuruwan su.
Gargaɗin shugabannin al'umma kan tsaro
Mista Dalyop ya bayyana cewa shugabannin al'umma sun riga sun bayar da rahoton zirga-zirgar mutanen da ba a yarda da su ba a dazuzzukan Gero da Rafin Bauna.

Source: Getty Images
Sun ce sun gargaɗi jami'an tsaro da sojoji a wani taron tsaro da aka yi kwanan nan, amma ba a ga wani canji ba.
Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin soja na gaggawa ba, ƴan ta'adda za su mamaye dukkan dazuzzukan jihar Filato nan ba daɗewa ba.
A halin yanzu, rundunar ƴan sanda ce kawai ta kai ɗauki bayan harin, inda suka kwashe wanda ya ji rauni zuwa asibiti yau.
Kokarin jin ta bakin kakakin ƴan sandan jihar Filato, Alfred Alabo, domin tabbatar da rahoton ya faskara domin bai ɗaga wayarsa ba zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng

