Babban Malami, Sheikh Isah Bauchi Ya Rasu, Bala Lau Ya Yi Ta'aziyya
- A ranar Juma'a, 4 ga watan Afrilun, 2026 aka wayi gari da rasuwar babban malamin Musulunci, Sheikh Isah Muhammad Bauchi
- Biyo bayan mutuwarsa, kungiyar Izala ta sanar da cewa an riga an gabatar masa da jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
- Shugaban Izala na Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi magana kan rasuwar malamin, inda ya bayyana irin gudunmuwar da ya bayar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Bauchi - An sanar da rasuwar babban malamin Musulunci, Alkali Sheikh Isah Muhammad Bauchi a ranar Juma'a, 4 ga watan Afrilun 2026.
Rahotanni sun nuna cewa malamai daga jihar Bauchi da sauran sassan Najeriya sun mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da kungiyar Izala.

Source: Facebook
Izala ta rasa malamin addini a Bauchi
Legit Hausa ta gano cewa kungiyar Izala ta jihar Bauchi ne ta sanar da rasuwar Sheikh Isah Muhammad Bauchi a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.
Sakon da ta wallafa a ranar Juma'a ya ce:
"Allah ya yi rasuwa wa Alkali Sheikh Isah Muhammad Bauchi."
Game da yi masa jana'iza kuma, kungiyar ta ce:
"Za a yi jana'iza da karfe 2:00 na rana a masallacin Juma'a na garin Miri, karamar hukumar Bauchi."
Ta kara da cewa:
"Muna addu'a Allah ya gafarta masa, ya sa aljannah ce makomarsa."
Bayanin Bala Lau kan rasuwar
Biyo bayan rasuwar, Sheikh Isah Muhammad Bauchi, kungiyar JIBWIS ta aike da sakon ta’aziyya ga 'yan uwa da abokan arzikin malamin.
Shafin Jibwis Nigeria ya wallafa a Facebook cewa:
"A madadin kungiyar Izala, shugaban Jibwis, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar Sheikh Isah Muhammad Bauchi.
"Wanda tuni aka yi masa jana'iza a masallacin juma'a na garin Miri, karamar hukumar Bauchi."
Gudunmuwar Sheikh Isah Bauchi
A sakon ta'aziyyar da ya fitar, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce Malamin ya ƙare rayuwarsa wajen karantar da al’umma addinin Musulunci.

Kara karanta wannan
Sojojin Isra'ila sun sha wuta a hannun mayakan Hezbollah, an tura da dama barzahu
Bala Lau ya ce:
"Tabbas wannan rashi babba ne a garemu, tare da sauran yan uwa da iyalansa."
Shugaban Izala na kasa ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa ya kyautata makwanci, ya bada hakuri ga ‘yan uwa da iyalai da shugaban JIBWIS na jihar Bauchi da sauran malamai a dukkan matakai.

Source: Facebook
Addu'ar da Sheikh Bala Lau ya yi
Sheikh Bala Lau ya yi addu'ar ubangiji ya gafarta masa kura-kuransa baki daya, Allah ya yi masa rahama, ya sa aljannar firdausi ce makomarsa tare da sauran musulmai da suka rasu.
Sauran al'ummar Musulmi sun yi wa Sheikh Isah Muhammad Bauchi addu'o'in samun rahama tun a lokacin sanar da rasuwar shi a kafafen sada zumunta.
An kaiwa malamin Musulunci hari
A wani labarin, kun ji cewa, Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya yi ikirarin cewa wani mutum ya nufi gidansa da niyyar kashe shi a Sototo.
Tun a kwanakin baya malamin ya nanata cewa akwai masu bibiyar shi domin su kashe shi, amma duk da haka ya shaida cewa babu ja da baya.
Mutumin da aka kama kuma ake zargi ya bayyana cewa daga karamar hukumar Yabo aka turo shi, amma wasu amsohin da ya bayar sun nuna alamun ba shi da hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
