Zaben 2027: Mace Ta Farko Ta Yi Murabus daga Mukamin Minista a Gwamnatin Tinubu
- Karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Barista Nkeiruka Onyejeocha, ta sanar da yin murabus daga mukaminta a yau Juma'a
- Onyejeocha ta mika sakon godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba ta na yin aiki a karkashin ajandar "Renewed Hope"
- Tsohuwar 'yar majalisar wakilan ba ta fito fili ta bayyana dalilin murabus din nata ba, amma ana zargin tana shirin yin takara a zaben 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Jerin ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu dake barin gado ya karu a yau Juma'a, 3 ga Afrilu, 2026.
Karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Barista Nkeiruka Onyejeocha, ta sanar da murabus dinta daga gwamnatin tarayya.

Source: Twitter
Ministar Tinubu ta yi murabus
Onyejeocha ta fitar da sanarwar murabus din ne ta shafinta na X, inda ta bayyana cewa ta bar ofishin ne da zuciya cike da godiya ga shugaban kasa da ma'aikatan da suka yi aiki tare da ita.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Shugaban Amurka, Trump ya 'kori' Antoni Janar ana tsaka da yakin Iran
Ta bayyana cewa yin aiki a matsayin minista babban gata ne da ya ba ta damar bayar da tata gudunmawar ga ci gaban kasar Najeriya.
A cikin jawabinta, tsohuwar 'yar majalisar wadda ta wakilci mazabar Isuikwuato/Umunneochi a jihar Abia, ta jinjina wa salon shugabancin Tinubu na hangen nesa.
"Yadda ka amince da ni da kuma goyon bayan da ka ba ni abin alfahari ne. Yin aiki a karkashin ajandar 'Renewed Hope' ya kasance babban daraja a gare ni. Na gode da ka yi imani da kwarewa ta wajen gina kasa."
- Barista Nkeiruka Onyejeocha.
Onyejeocha ta gode wa tsofaffin abokan aikinta
Hakazalika, tsohuwar ministar godewa sakataren dindindin, daraktoci, da daukacin ma'aikatan ma'aikatar kwadago bisa jajircewarsu wajen kare hakkin ma'aikata da inganta tsaron wuraren aiki a fadin Najeriya.
Onyejeocha ta bayyana cewa:
"A tare, mun samar da tsare-tsare da suka kare 'yancin ma'aikata, suka samar da yanayin aiki mai kyau, kuma suka samar da damarmakin aiki masu yawa."
Karanta sanarwar a nan kasa:

Source: Twitter
Makomar siyasar ministar da ta yi murabus
Duk da cewa wasu ministoci sun yi murabus domin shiga takara a zaben 2027, Barista Onyejeocha ba ta fito fili ta bayyana cewa za ta yi takara ba, a cewar rahoton PM News.
Sai dai ta ba da rahoton cewa murabus dinta ba shi ne karshen aikinta ga Najeriya ba, face wani sabon babi ne da aka bude na hidimta wa al'umma.
Masu lura da al'amuran siyasa na ganin cewa Onyejeocha na iya komawa jiharta ta Abia domin fuskantar kalubalen siyasa na gaba, duba da yadda ta bayyana cewa mazaunanta ne kashin bayan karfinta.
Ta jaddada cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen ginin Najeriyar da kowa yake mafarki a koda yaushe yau.
Ministan sufurin Najeriya ya yi murabus
Tun da fari, mun ruwaito cewa, ministan sufuri, Sa’idu Alkali ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Bola Tinubu a yau Talata, inda ake zargin zai tsaya takarar gwamna.
Murabus din yana karkashin umarnin da shugaban kasa ya bayar cewa dukkan masu rike da mukaman siyasa su sauka kafin karshen Maris, 2026.
Sa’idu Alkali ya bi sahu Yusuf Tuggar da Yusuf Sununu wadanda suma suka yi murabus domin neman wasu kujerun a zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng
