An Je Gidan Malamin Musulunci da zai Nemi Gwamna za a Kashe Shi
- Malamin Musulunci, Sheikh Bashir Sani Ahmed ya fitar da sanarwa cewa an kama wani matashi da ya je gidan shi domin kashe shi a Sokoto
- An kama matashin kafin ya yi nasara, inda jama'a suka rika masa tambayoyi kafin daga bisani a mika shi ga rundunar 'yan sandan jihar
- Tun a kwanakin baya malamin ya sha bayyana cewa ana masa barazanar kisa, inda ya bayar da labarin cewa ya hango wani mutum a gidan shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Bayan shafe lokaci yana cewa ana masa barazar kisa, Bashir Ahmad Sani Sokoto ya sanar da cewa an kama wanda ya zo zai kashe shi.
Sheikh Bashir Sokoto na daya daga cikin malaman addinin Musulunci da suka fito karara suka bayyana cewa za su nemi takarar gwamna a zaben 2027 mai zuwa.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya yi kan kama wanda ake zargin ne a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook.
An kama wanda zai kashe malamin Musulunci
A bidiyon da malami ya wallafa, an yi wa wanda ake zargin tambayoyi kan kan cewa daga ina ya fito yayin da ake zaton ya zo kashe malamin.
Daga aka tambaye shi daga ina ya ke, ya ce:
"Daga Yabo,'
An kara masa tambaya kan wa ya turo shi, sai ya ce:
"Sani Yabo, Tambar Yabo, da baba na, sai mahaifiyata, sai kani na."
Masu masa tambayoyi a bidiyon sun bukaci ya musu bayanai mai kyau, inda suka ce ya raina musu hankali saboda irin amsar da ya ke ba su.
Wanda aka kaman ya ciro katin dan kasa a aljihun shi, inda ya rika cewa a kira jami'an 'yan sanda kuma jama'a suka tabbatar da an kira su.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Shugaban Amurka, Trump ya 'kori' Antoni Janar ana tsaka da yakin Iran
Daga karshe ya fara karanta wasu ayoyin Kur'ani mai girma amma mutane suna cewa karatun da ya ke yi ba zai masa wani amfani ba.

Source: Facebook
An mika matashin wajen 'yan sanda
Biyo bayan tambayoyin da mutane da dama suka masa a bidiyon, malamin ya sanar da cewa an mika mutumin wajen 'yan sanda.
Ya ce:
"Yanzu haka mun kai shi wajen yan sanda ofishin CID kuma tuni an fara bincike a gano wadanda suka saka shi.
Allah ya tsare mana malam da tsarewar sa."
An kai hari gidan malamin a Ramadan
A wani labarin, mun kawo muku cewa a farkon azumin watan Ramadan da ya gabata, Sheikh Bashir Sokoto ya bayar da labarin cewa an kai masa hari domi halaka shi jim kadan bayan shan ruwa.
Ya sanar da cewa ya hango wani mutumi a cikin gidansa a lokacin da ya ke shirin buda baki amma kuma babu gudu ba ja da baya a kan abubuwan da ya saka a gaba.
Bayanin da ya yi a wancan lokacin ya nuna cewa masu neman kashe shi sun makara, inda ya ce sun yi sake dan zaki ya girma kuma ya ce zai yi karin bayani a gaba.
Asali: Legit.ng
