Bayan Ministoci Sun Yi Murabus, Tinubu Ya Yi Sababbin Nade Nade a Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa domin inganta harkokin mulki a Najeriya
- Shugaban nada sabon shugaban hukumar kula da kasuwancin kasa watau NCX tare da sabon kwamitin gudanarwa
- Nadin ya zo ne domin karfafa kasuwar hada-hadar kayayyaki, inganta fitar da kayayyakin noma waje, da bunkasa tattalin arzikin da ba na mai ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kwana biyu bayan rasa wasu masu mukamai a gwamnatinsa, Bola Tinubu ya yi sababbin nade-nade.
Shugaban Tinubu ya amince da nadin Dalhatu Abubakar a matsayin shugaban hukumar kula da kasuwancin kasa, NCX.

Source: Twitter
A wata sanarwa daga fadar shugaban kasa da aka wallafa a shafinta na X, an ce sake fasalin kwamitin ya yi daidai da manufofin sabuwar fata da ke mayar da hankali kan wadatar abinci.
Dan Arewa ya samu muƙamin shugaban CAC
Hakan ya biyo bayan nadin da Bola Tinubu ya yi na Sanata Ibrahim Ida a ranar Talata 31 ga watan Maris, 2026.
Shugaba Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar yi wa kamfanoni rajista (CAC) wanda ake da ran zai inganta hukumar.
Tinubu ya nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin wanda zai shugabanci hukumar CAC domin inganta harkokin kasuwanci.
An nada Dalhatu shugaban hukumar NCE
Nadin ya fara aiki nan take, kuma wani bangare ne na kokarin gwamnati na karfafa tsarin kasuwancin kayayyaki da bunkasa fitar da kayayyakin noma zuwa kasashen waje.
Sanarwar ta ce nadin zai taimaka wajen inganta gano farashi, kara gaskiya a kasuwa, da fadada damar fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin duniya.
Sababbin mambobin kwamitin sun hada da Najah Muhammed, Bamidele Hussein, Mezuo Nwuneli, Obi Igwe, Foluso Ayo-Olaiya, da Anthony Atuche a matsayin manajan darakta.

Source: Twitter
Aikin da sabon kwamitin zai yi
Fadar shugaban kasa ta ce sabon kwamitin zai samar da jagoranci mai kyau domin cikakken farfado da cibiyar da kuma jawo masu zuba jari.

Kara karanta wannan
2027: Jerin ministoci da manyan jami’an gwamnatin Tinubu 7 da suka yi murabus don takara
Za a mayar da hankali kan bangarorin ajiya, sufuri, da gine-ginen kasuwanci domin bunkasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi.
Gwamnati ta ce wannan cibiyar na da muhimmanci wajen cimma manufofin wadatar abinci da rage dogaro da man fetur a tattalin arziki.
Ta hanyar tsarin kasuwanci mai kyau da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, za a inganta bin diddigin kayayyaki da daidaita kasuwanni.
Dalhatu Abubakar dan kasuwa ne daga Kano, kuma shugaban kamfanin Al-Hamsad Integrated Rice Mills tare da jagorantar CONSCCIMA a baya.
An kuma bayyana shi a matsayin tsohon shugaban KACCIMA, wanda ya taka rawar gani wajen bunkasa harkokin noma da horar da ‘yan kasuwa a Arewacin Najeriya.
Minista ya sake murabus a gwamnatin Tinubu
A baya, mun ba ku labarin cewa ministan sufuri, Sa’idu Alkali ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Bola Tinubu da ake zargin zargin zai tsaya takarar gwamna.
Murabus din yana karkashin umarnin da shugaban kasa ya bayar cewa dukkan masu rike da mukaman siyasa su sauka kafin karshen Maris, 2026.
Sa’idu Alkali ya bi sahu Yusuf Tuggar da Yusuf Sununu wadanda suma suka yi murabus domin neman wasu kujerun a zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng
