An Kama Sojan Bogi a Jos yayin da Ake Kashe Kashe a Filato

An Kama Sojan Bogi a Jos yayin da Ake Kashe Kashe a Filato

  • Rundunar 'yan sandan jihar Filato ta yi karin haske kan matakan da ta ke dauka kan sabon rikicin da ya barke bayan wani hari da aka kai
  • Kakakin 'yan sandan jihar, Alfred Alabo ya sanar da cewa jami'an rundunar sun kama wani sojan bogi yayin wani samame da suka kai
  • An yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu, su ba jami'an tsaro hadin kai yayin da hukumomi ke kokarin dawo da zaman lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Plateau ta tabbatar da kama wani da ake zargi da zama sojan bogi tare da wasu mutum biyar dangane da tashin hankalin da ya faru a wasu sassan Jos a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Abin da Ministan tsaro ya fada wa sojojin da ke arangama da 'yan ta'adda a Borno

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Alfred Alabo, ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta waya bayan barkewar rikici a wasu sassan jihar.

Taswirar jihar Filato
Taswirar jihar Filato a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Rahoton tashar Channels TV ya nuna cewa rundunar 'yan sanda ta bukaci hadin kan al'umma yayin da take kokarin dawo da zaman lafiya.

An kama sojan bogi a garin Jos

Kakakin 'yan sanda ya ce an kama mutumin sanye da singileti irin ta sojoji da wata riga a unguwar Rukuba, wajen da aka kashe mutane 28 tare da jikkata wasu 22 a harin da aka kai da dare.

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne yayin da yake yawo a yankin da rana, inda aka same shi da katin shaidar makarantar soja ta Najeriya (NMS) na bogi.

Alabo ya kuma bayyana cewa an kama wasu mutum biyar a sassa daban-daban na birnin Jos dangane da rikicin da ya faru a ranar, yana mai cewa su ‘yan daba ne da suka yi amfani da yanayin rikicin wajen aikata laifuffuka.

Ya ce:

“Barayi ne da suka yi anfani da tashin hankalin wajen kwace jakunkuna da kuɗi daga hannun jama’a, musamman a yankin Terminus.”

Kara karanta wannan

Amurka ta ci karo da cikas, Iran ta illata ta a yakinta da kasar Isra'ila

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, rundunar 'yan sandan jihar ta sanar da kama wani matashi dauke da bindigogi biyu.

Matakin da 'yan sanda suka dauka

Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun gaggauta shiga tsakani a lokacin da rikicin ya fara, inda suka fatattaki ‘yan daban tare da dawo da zaman lafiya.

Gwamna Caleb Mutfwang
Caleb Mutfwang a wajen da aka kai hari a Filato. Hoto: Government of Plateau State
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto ya ce an ƙara tsaurara matakan tsaro a muhimman wurare ciki har da yankin jami’ar jihar da sauran wurare masu muhimmanci domin kare rayuka da dukiyoyi.

Alabo ya buƙaci al’umma da su kasance cikin natsuwa amma su ci gaba da lura, tare da kira ga jama’a su riƙa kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an tsaro.

An kashe Musulmai 4 a Filato

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta sanar da irin barnar da aka yi wa Musulmai a harin da aka kai Filato.

Kungiyar ta ce akalla mutum hudu ne aka kashe cikin Musulmai yayin da wasu suke kwance a asibiti suna karkashin kulawar likitoci.

Baya ga kisan da aka yi, kungiyar Jama'atu ta sanar da cewa an nemi wasu Musulmai 10 an rasa, kuma har yanzu ba a gano a ina suke ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng