Ma'aikata Za Su Yi Kwanaki 2 ba Su Je Ofis ba, Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Juma’a, 3 da Litinin, 6 ga Afrilu, 2026, a matsayin ranakun hutu domin bikin Good Friday da Easter Monday
- Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin wajen yin tunani kan soyayyar da Yesu Almasihu ya nuna
- Wata mabiyar addinin Kirista a jihar Bauchi, Magdalene Apollos, ta ce za su sanya Najeriya a cikin addu'o'in neman zaman lafiya a bikin Easter na bana
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun Juma’a da Litinin, 3 da 6 ga Afrilu, 2026, a matsayin ranakun hutun bikin Easter da Good Friday.
Hakan zai sanya rufe ma'aikatu a ranakun domin samun damar yin bikin da Kiristoci ke gudanarwa duk shekara.

Source: Twitter
Gwamnati ta bada hutun kwanaki 2
Rahoton BBC ya nuna cewa an samu bayanai kan hutun kwanaki biyu da gwamnatin Najeriya ta bayar ne a wata sanarwa da ma'aikatar cikin gida ta fitar ranar Laraba, 1 ga Afrilu, 2026.
Sanarwar ta fito ne daga bakin ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, a madadin gwamnatin tarayya, inda ya mika sakon taya murna ga dukkan Kiristoci a fadin Najeriya.
Babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, wacce ta sanya hannu kan sanarwar, ta bukaci ‘yan kasa da su dauki lokacin bikin a matsayin dama don yin aiki da darasin sadaukarwa da soyayya da Yesu Kiristi ya koyar.
An bukaci yin addu'a a lokacin Easter
Minista Tunji-Ojo ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin hutun wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a kasar nan.
Ya jaddada cewa Najeriya na bukatar hadin kan jama’a a kowane lokaci musamman a irin wannan lokaci da ake bukatar sada zumunci da rungumar juna ba tare da bambanci ba.
Jaridar Vanguard ta rahoto Tunji-Ojo yana cewa:
"Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tafiya a kan turbar daukar matakan da za su kawo hadin kan kasa da ci gaban tattalin arziki."
Legit ta tattauna da Magdalene Apollos
Wata mabiyar addinin Kirista a jihar Bauchi, Magdalene Apollos ta bayyana wa Legit Hausa cewa za ta yi amfani da lokacin Easter wajen sada zumunci da bada sadaka ga mabukata.

Source: Getty Images
Magdalene, wacce daliba ce a kwalejin fasaha ta tarayya da ke Bauchi, ta ce:
"Allah ya kawo mu shekara ta kawo mu, yanzu dai muna shirye shiryen bikin Easter, kuma ni da 'yan gidanmu mun shirya zuwa coci, don yin addu'o'i, da nuna godiya da samun Yesu, mai cetonmu.
"Wannan biki ne na kasancewa cikin 'yan uwa da malamanmu. Kuma za mu yi wa kasar mu addu'a, ubangiji Allah ya ba mu zaman lafiya, musamman fadace fadacen da ake yi a Jos da sauran wurare, Allah ya kawo mana karshen su."
Minista ya cika baki kan tazarcen Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo, ya bugi kirji kan cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasara a zaben 2027.
Tunji-Ojo ya ba da tabbacin ne yayin da yake karɓar tawagar tallata Tinubu ta GMT karkashin jagorancin daraktanta, Hon. Bayowa Foresythe a ofishinsa da ke Abuja.
Ministan ya jaddada kudurinsa na goyon bayan shirye-shiryen wayar da kan jama’a da kuma ayyukan da za su karfafa nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng


