Barayo Ya Shiga Dakin Matar Sarki Sanusi II Ya Sace Kayan Naira Miliyan 60
- Wata kotu a jihar Kano ta tura mai tuka matar Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II kan zargin shiga har dakinta ya tafka sata
- Rahotanni sun nuna cewa an zargi matukin motar da shiga dakin matar ba tare da izini ba da hada kai da wasu mutane waje tafka mata sata
- Bayan sauraron karar da aka shigar a gaban kotun da ke Nomansland, wanda ake zargi ya amince da laifinsa sannan an daga shari'ar zuwa gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rahotanni da suka fito daga jihar Kano sun nuna cewa wata kotu ta tsare direban matar Sarki Muhammadu Sanusi II kan zargin satar kayan ado.
Hakan ya biyo bayan wani bincike da aka gudanar da ba a ga kayan ba, kuma aka zargi matukin motar da yin gaba da su, lamarin da ya kai ga zuwa kotu.

Source: Original
Barawo ya yi wa matar Sarki sata
Daily Trust ta wallafa cewa kotun majistare da ke zama a Nomansland, a ƙaramar hukumar Fagge ta jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare wani direba tare da wasu mutum biyu.
Rahotanni sun nuna cewa an tsare su ne bisa zargin satar kayan ado, kuɗi da kuma wayar hannu mallakin matar sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
An gurfanar da waɗanda ake zargi, Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini, bisa tuhume-tuhume uku da suka haɗa da haɗa baki, sata da kuma karɓar kayan sata.
Bayanin da lauyan gwamnati ya yi
Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Abubakar Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa Sulaiman Yakubu, wanda ke aiki a matsayin direban matar sarkin, ya shiga ɗakinta ba tare da izini ba ya yi sata.
Barista Abubakar Ibrahim ya yi zargin cewa ya sace kayan ado da aka kiyasta darajarsu ta kai Naira miliyan 60, tare da kuɗi da wayar hannu.
Lokacin da aka karanta musu tuhumar, Sulaiman ya amsa laifinsa a kan dukkan tuhume-tuhumen, yayin da sauran biyu suka musanta zargin.
An nemi belin barawon matar Sarki
Rahoton Sahara Reporters ya nuna cewa bayan gabatar da korafi, lauyan waɗanda ake ƙara, Barista A.A. Abdullahi, ya shigar da buƙatar beli a gaban kotu
A hukuncinsa, Alkalin kotun, Halilu Abdurahman, ya amince da bayar da beli ga waɗanda ake zargin tare da sharuda, ciki har da gabatar da wanda zai tsaya musu wanda dole ne ya kasance uba ko ɗan’uwa.

Source: Twitter
Haka zalika dole mai tsaya musu ya kasance ma’aikacin gwamnati da ba ya ƙasa da mataki na 15, tare da biyan kuɗin beli na Naira miliyan 10 ga kowannensu.
An ɗage shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu domin ci gaba da sauraron ta, yayin da aka ci gaba da tsare waɗanda ake zargin har sai sun cika sharudan belin.
Sanusi II ya saka bakin rawani
A wani labarin, kun ji cewa mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi shiga da bakin rawani a watan Ramadan da ya wuce.
Sarkin ya bayyana cewa yana sanya bakin rawani ne domin tunawa da wani abu da ya faru da Annabi Muhammad SAW a Makka.
Bisa al'ada, Khalifa Muhammadu Sanusi II yana sanya rawanin ne domin a cewarsa, Annabi SAW ya sanya kalarsa a lokacin bude garin Makka.
Asali: Legit.ng


