Matakin da Alkali Ya Dauka kan Bukatar Beli a Shari'ar El Rufai da Hukumar ICPC

Matakin da Alkali Ya Dauka kan Bukatar Beli a Shari'ar El Rufai da Hukumar ICPC

  • Babbar kotun tarayya dake Kaduna ta dage sauraron bukatar belin tsohon gwamna Nasir El-Rufai a shari'arsa da hukumar ICPC
  • Jami'an hukumar ICPC sun tafi da tsohon gwamnan cikin wata mota kirar Hilux bayan kammala zaman kotun dake cike da tsaro yau
  • Baya ga kotun tarayya, an kuma gurfanar da El-Rufai a gaban babbar kotun jiha dake Kawo kan shari'ar da ke da alaka da rashawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Babbar kotun tarayya dake birnin Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar belin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, zuwa ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2026.

Wannan mataki ya biyo bayan zaman kotun da aka gudanar a yau Talata ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, lamarin da ke nuna muhimmancin wannan shari'a ta zargin almundahana da ake yi wa El-Rufai.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya gurfana a kotu ana jimamin rasuwar mahaifiyarsa

Kotu ta dage sauraron bukatar bada belin El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai a lokacin da ya isa harabar babbar kotun Kaduna tare da jami'an ICPC. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

An dage sauraron bukatar belin El-Rufai

Lauyan tsohon gwamnan, Ukpong Akpan, ya tabbatar da wannan ƙarin lokaci, inda jaridar The Punch ta ruwaito shi yana fadawa 'yan jarida cewa:

"Ina ba ku haƙuri, ba zan iya magana yanzu ba domin muna tsaka da aiki, dole ne in tafi in shigar da martaninmu yau.
"Amma dai an dage sauraron bukatar belin zuwa gobe (Laraba)."

Jim kaɗan bayan ɗage zaman kotun, jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na ICPC sun fito da El-Rufai daga harabar kotun cikin wata farar mota kirar Hilux.

Nasir El-Rufai dai yana fuskantar shari'a ne a gaban Mai shari'a Rilwan M. Aikawa kan zargin karkatar da dukiyar al'umma da kuma halatta kuɗaɗen haram lokacin yana gwamna.

An gurfanar da El-Rufai a wata kotu

Baya ga shari'ar dake gaban kotun tarayya, an kuma gurfanar da El-Rufai a gaban babbar kotun jihar Kaduna dake mazaunar ta a Kawo a yau Talata kan wasu zarge-zarge daban-daban.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda yakin Iran da Amurka ya shafi tattalin arziki da tsaron Najeriya

A wannan kotun, an gurfanar da shi tare da wani mutum mai suna Amadu Sule, inda ake zarginsu da amfani da ofis ta hanyar da ba ta dace ba da kuma damfara.

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa waɗannan tuhume-tuhume na daban ne da waɗanda suke gaban babban kotun tarayya, kuma duka hukumar ICPC ce ta shigar da su.

Kotu ta sanya Laraba a matsayin ranar da za ta saurari bukatar belin El-Rufai.
Malam Nasir El-Rufai na fitowa daga motar hukumar ICPC da aka isa kotu a Kaduna. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Komawar El-Rufai hannun ICPC bayan jana'iza

Tsohon gwamnan ya shafe sama da wata guda a tsare kafin a kawo shi kotu, matakin da ya janyo ce-ce-ku-ce sosai a tsakanin 'yan Najeriya a faɗin ƙasar nan.

Ko da yake hukumar ta ICPC ta sake shi a ranar 27 ga Maris domin ya halarci jana'izar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, rahoto ya nuna cewa ya koma hannun hukumar yau.

Kotun ta riga ta sa ranar 31 ga Maris, 2026, domin sauraron dukkan buƙatun dake gabanta, ciki har da neman belin sa wanda za a ci gaba da shi a gobe Laraba.

El-Rufai ya sauke Alkur'ani a ICPC

A wani labari, mun ruwaito cewa, wani makusancin Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana yadda abokinsa ya rika ribatar lokacin da hukumar ICPC ta ke tsare da shi.

Kara karanta wannan

Trump na cikin yaki da Iran, gagarumar matsala ta tunkaro shi a Amurka

An gano cewa tsohon gwamnan ya dukufa, inda kammala sauke Alƙur’ani mai tsarki tare da karanta littattafai 10 yayin da ya ke hannun hukumar.

Nasir El-Rufa'i na tsareva hannun ICPC, sai da an sako shi wucin gadi domin ya halarci jana'izar mahaifiyarsa tare da karban gaisuwa wajen makoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com