Kisan Gilla a Jos Ya Dauki Hankalin Amurka, Dan Majalisa Ya Shawarci Tinubu
- Dan majalisa daga Amurka, Riley Moore ya yi magana kan harin da aka kai a Jos a ranar Lahadi 29 ga watan Maris, 2026
- Moore ya soki hare-haren da aka kai wa Kiristoci a Jos, ya bukaci Najeriya ta ƙarfafa tsaro domin kare lafiyar al'ummar kasar
- Ya gargadi cewa ci gaba da kashe-kashe na iya lalata dangantakar diflomasiyya tsakanin Amurka da Nigeria
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Wani dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi kakkausar suka kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya.
Moore ya yi gargadin cewa harin da aka kai a Jos na iya janyo matsala a dangantaka tsakanin kasar Amurka da Nigeria ta bangarori da dama.

Source: UGC
Kisan Jos: Martanin dan majalisar Amurka
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Moore ya bayyana kashe-kashen a matsayin wani abin damuwa, bayan rahoton cewa an kashe akalla Kiristoci 10 a Anguwan Rukuba da ke Jos, a ranar 'Palm Sunday'.
Ya ce irin wadannan hare-hare sun zama ruwan dare a lokutan bukukuwan addini, yana mai cewa dole ne hukumomin Najeriya su dauki matakai masu tsauri domin dakile zubar da jini a nan gaba.
Moore ya ce:
“A wannan rana ta 'Palm Sunday', rahotanni daga Najeriya sun nuna cewa an kashe akalla Kiristoci 10 a birnin Jos.
‘Yan ta’adda sun bude masu wuta kafin su sare su da adduna, abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba.”

Source: Twitter
Shawarar Moore ga gwamnatin Bola Tinubu
Moore ya kara da cewa irin wannan hari yana daga cikin jerin hare-haren da ake kai wa Kiristoci a ranakun bukukuwan addini, yana mai zargin cewa irin wadannan abubuwa na faruwa akai-akai a Najeriya.
Dan majalisar ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara tsaurara matakan tsaro kafin bukukuwan 'Triduum da Easter', yana mai gargadin cewa rashin daukar mataki zai iya haifar da mummunan sakamako a dangantakar kasashen biyu.
Ya ce:
“Dole ne gwamnati ta dauki wannan barazana da muhimmanci, ta kuma tashi tsaye wajen kare rayukan Kiristoci, in ba haka ba hakan na iya jawo babbar matsala a dangantakar Najeriya da Amurka.”
Rahotanni sun nuna cewa jihohin yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma na fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin dauke da makamai a baya-bayan nan.
Ganin dan Amurka ya jawo magana a Plateau
Mun ba ku labarin cewa masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun fara magana kan wani dan kasar Amurka, Alex Birbir da ke yawo a kauyukan jihar Plateau.
Rahotanni sun nuna cewa Alex Birbir na shiga kauyuka ne a jihohin Arewa ta Tsakiyan Najeriya da sunan wa'azi da wayar kan Kiristoci musamman kan matsalolin tsaro.
Yawon da Alex Birbir ke yi ya fara daukar hankali ne bayan ganin shi a wajen da aka kai hari aka kashe mutane da dama a cikin dare a birnin Jos da ke jihar Plateau.
Asali: Legit.ng

