Jami'an Tsaro da Mutanen Kauyen Kano Sun Gwabza, An Rasa Rayuka da Dama

Jami'an Tsaro da Mutanen Kauyen Kano Sun Gwabza, An Rasa Rayuka da Dama

  • Ana fargabar mutane da dama sun mutu sakamakon rikici tsakanin jami’an tsaro da mazauna wasu ƙauyuka a Kano
  • Rahotanni sun bayana cewa rikicin ya samo asali ne daga takaddamar filaye tsakanin mazauna da wani shugaban Fulani
  • An kona gidaje tare da tilasta wa mutane da dama tserewa daga muhallansu yayin da tsofaffi suka samu raunuka da konuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Ana fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukansu, yayin da dukiyoyi suka salwanta sakamakon wani rikici mai muni a Wudil

Tashin hankali ya ɓarke tsakanin jami’an tsaro da mazauna ƙauyukan Katai da Fauda da ke ƙaramar hukumar Wudil a jihar Kano.

An samu rikici tsakanin jami'an tsaro da mutanen wasu kauyuka
Taswirar jihar Kano, inda aka gwabza tsakanin mutanen gari da yan sandan Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga wata takaddama ta fili tsakanin wasu mazauna ƙauyen da wani shugaban gargajiyar Fulani.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi murabus daga harkokin siyasa? Gaskiyar zance ta fito

Yadda aka fara rikici a Kano

Mazauna garuruwan sun ce takaddamar ta faru saboda Shugaban Fulanin, wanda ake zargin ya yi iƙirarin mallakar wasu filaye da Hausawa ‘yan asalin yankin ke cewa nasu ne.

Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya fara ƙamari ne bayan da mazauna ƙauyen suka ƙi amincewa da barin filayen da ake takaddama a kai.

Lamarin ya kara taɓarɓarewa ne bayan wani samame da aka ce wasu dauke da makamai suka kai cikin dare zuwa garuruwansu.

Shaidun gani da ido sun ce maharan, waɗanda ke sanye da kayan farar hula, sun kutsa cikin ƙauyukan tare da bude wuta.

Ana zargin an gwabza ne bayan an harbi mutum daya a a Kano
Sufeton yan sandan Najeriya, Tunji Disu a wani karamin taro Hoto: Nigerian Police Force
Source: Twitter

An ce lamarin da ya jefa mutane a cikin firgici, inda da farko suka ɗauka ‘yan bindiga ne suka kai harin.

A cewar wasu mazauna, sun yi gaggawar tattaruwa da makaman gargajiya domin kare kansu, wanda ya haifar da arangama mai zafi.

An yi asarar rai a Kano

Rahotanni sun ce mazauna ƙauyen sun yi nasarar cafke ɗaya daga cikin maharan tare da kashe shi, suna zaton ɗan bindiga ne bayan sun harbi mutum guda a yankin.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Koriya ta yi gwajin injin makami mai linzami da zai iya kaiwa Amurka

Daga baya ne aka tabbatar cewa mutumin da aka kashe jami’in tsaro ne, lamarin da ya kara dagula al’amura tare da jefa yankin cikin sabon tashin hankali.

Majiyoyi sun kuma zargi cewa jami’an tsaro sun kaddamar da wani farmakin ramuwar gayya, wanda ya jawo karin asarar rayuka da kuma kona gidaje.

Harin da jami'an tsaron suka kaddamar ya jawo asarar rayuka, abin da ya tilasta wa mazauna yankin da dama tserewa domin tsira da rayukansu.

Shugaban ƙaramar hukumar Wudil, Abba Muhammad Tukur, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici matuka. A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Abba Darki ya fitar, ya tabbatar wa da mazauna yankin cewa ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

APC ta musanta kai farmaki a Kano

A wani labarin, za a ji cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta musanta zargin cewa tana da hannu a harin da aka ce an kai wa ‘yan NNPP a taron da suka yi a Kano.

Jam’iyyar ta ce zargin ba shi da tushe, kuma tana hasashen yana da nasaba da rikicin cikin gida na NNPP kai tsaye amma babu hannunta ko na magoya baya a lamarin.

Jam'iyya mai mulki ta APC ta goyi bayan a yi gaggawar gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin domin a hukunta mutanen da suka kai harin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng