Tinubu Ya Yi Abun Mamaki, Ya Sadaukar da Dukkan Albashinsa na Shekaru 3 ga Sojoji
- Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude asusu na musamman domin tallafawa sojoji da iyalansu yayin da ya cika shekaru 74
- Domin bada tasa gudunmawar, Tinubu ya sadaukar da dukkan albashin da ya karba tun daga lokacin da ya hau mulki a 2023
- Tinubu ya nemi gwamnoni, 'yan majalisa da masu hannu da shuni da su bada tasu gudunmawar domin tallafawa dakarun kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sanar da samar da wani asusu na musamman domin tallafawa sojojin Najeriya, musamman waɗanda suka ji rauni da kuma iyalan jaruman da suka rasu.
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ba da umarnin gaggawa ga Akanta Janar na ƙasa domin buɗe wannan asusu a hukumance.

Source: Twitter
Tinubu ya sadaukar da dukkan albshinsa
A cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa:
"A wannan zagayowar ranar haihuwata ta shekaru 74, ina jinjina wa jajirtattun maza da mata na rundunar sojinmu waɗanda ke kare ƙasarmu."
Domin zama misali, Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin bayar da dukkan albashin da ya karɓa tun lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa domin fara gudanar da wannan asusu.
"A matsayin tawa gudunmawar, na sadaukar da dukkan albashina tun daga lokacin da na hau mulki, za a sanya su cikin wannan asusu a matsayin kuɗin somin-tabi ga wannan shiri."
Tinubu ya nemi goyon bayan gwamnoni
Baya ga gudunmawar da ya bayar, shugaban ya yi kira ga gwamnonin jihohi, 'yan majalisar tarayya, da kuma ’yan kasuwa da su ba da tasu gudunmawar.
Tinubu ya bayyana cewa:
"Ina kiran gwamnoninmu, 'yan majalisar tarayya, 'yan kasuwa, abokaina da duk masu fatan alheri da su mara wa wannan gagarumin shiri baya."
Ya ba da tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba za a bayyana wa jama'a dukkan bayanan asusun domin kowa ya samu damar bayar da gudunmawar sa ga jaruman ƙasar nan.

Source: Twitter
Tinubu ya tunatar da 'yan Najeriya
Shugaba Tinubu ya jaddada buƙatar ƙasa ta rinka girmama sadaukarwar da jami'an soji da iyalansu suke yi domin tabbatar da zaman lafiyar daukacin 'yan Najeriya.
Ya yi nuni da cewa:
"Kada mu taba manta wa da waɗanda suke jefa rayukansu cikin haɗari domin zaman lafiyarmu, ko kuma sadaukarwar da iyalansu suke yi a kullum.
"Wannan ba sadaka ba ce; wannan nauyi ne dake kanmu, kuma za mu tabbatar da cewa mun sauke wannan nauyin domin gina makoma mai kyau."
Karanta rahoton a nan kasa:
Tinubu ya amince a kara albashin sojoji
A wani labari, mun ruwaito cewa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙarin albashi ga dukkan sojojin Najeriya.
Laftanal Shaibu ya ce Tinubu ya kuma amince da ƙarin alawus-alawus ga dakarun dake gadin fadar shugaban ƙasa domin nuna jin daɗi ga ƙwazonsu.
Baya ga batun albashi, Laftanar Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya amince da ɗaukar sababbin dakarun sojoji guda 28,000.
Asali: Legit.ng

