'Ina Neman Afuwa': Ɗan Nasir El Rufai Ya ba Shettima Hakuri kan Rubutu a Kansa

'Ina Neman Afuwa': Ɗan Nasir El Rufai Ya ba Shettima Hakuri kan Rubutu a Kansa

  • Dan tsohon gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai, ya nemi afuwa ga mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima kan kalamansa
  • Ya ce sakon nasa kuskure ne kuma wanda dacewa, yana mai jaddada cewa yana girmama Shettima, tare da musanta cewa an tilasta masa janye kalaman
  • Lamarin ya zo ne yayin da ake rikicin siyasa da ya shafi Nasir El-Rufai, wanda ake tuhuma da rashawa kuma aka gurfanar da shi a kotu Kaduna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Bashir El-Rufai, dan tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya nemi afuwa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Wannan ya biyo bayan wallafa wani sako Da ya yi da ya ke sukar Kashim Shettima a matsayin marar tasiri.

Bashir El-Rufai ya nemi afuwar Shettima
Dan tsohon gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai da Kashim Shettima. Hoto: @BashirElRufai, Kashim Shettima.
Source: Twitter

Dan El-Rufai ya nemi afuwar Shettima

Hakan na cikin wani sako da ya wallafa a X a yau Lahadi 29 ga watan Maris din shekarar 2026.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri: Cikin jimami, ISWAP ta sanar da mutuwar babban kwamandanta

A cikin sakon, Bashir ya bayyana cewa kalamansa na baya sun kasance kuskure kuma marasa dacewa, yana mai cewa yana girmama Shettima sosai.

Ya bayyana cewa yana girmama mataimakin shugaban kasar kuma yana mutunta shi fiye da kima.

Ya ce:

"Ina so in yi amfani da wannan dama domin in nemi afuwar Mataimakin Shugaban Najeriya, Mai girma Kashim Shettima, bisa tsohon sakona da na kira shi marar ƙarfi.
"Shi mutum ne da nake matuƙar girmamawa da kuma nake mutuntawa amma na yi kuskure bisa rubutun da na yi.
" Wancan rubutu na rashin tunani ne da na yi ba tare da lura ba."
Dan El-Rufai ya fadi yadda yake kallon Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayin taro a Abuja. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Sakon da Bashir El-Rufai ya rubuta a baya

A cikin asalin sakon da ya wallafa a ranar 6 ga Maris, 2026, wanda daga bisani ya goge, Bashir El-Rufai ya bukaci Shettima ya dauki mataki mai tsauri kan zargin cin hanci da rashawa a Fadar Shugaban Kasa.

Ya rubuta cewa:

“Ina son Shettima. Amma abin takaici, ba shi da jajircewa kwata-kwata.
“Ina fatan wata rana zai gane cewa yana a wani matsayi na musamman, kuma yana da ikon rusa gaba ɗaya tsarin dangin masu cin hanci da laifi a Villa, a gaskiya yana da damar yin hakan.”

Kara karanta wannan

Aminu Gwarzo: "Abin da yasa na hakura da kujerar Mataimakin gwamnan Kano"

Bayan neman afuwar, mutane sun yi martani daban-daban, wasu na yabawa, wasu na sukar sa, amma ya ce babu wata barazana da aka yi masa.

Lamarin ya biyo bayan rikicin siyasa da ya shafi mahaifinsa, wanda ake zargi da rashawa da badakalar kudi, kuma aka gurfanar da shi a kotu Kaduna.

Bashir El-Rufai ya sace guiwar Uba Sani

Mun ba ku labarin cewa a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026 aka sanar da rasuwar mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya aika da sakon ta'aziyya ga El-Rufai kan rasuwar Hajiya Umma El-Rufai da ta bar duniya bayan fama da jinya.

Sai dai, jim kadan bayan fitar da sakon ta'aziyyar, wani dan El-Rufai watau Bashir El-Rufai, ya yi masa martani mai zafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.