Yadda El Rufa'i Ya Sauke Alkur'ani, Ya Karance Littafai 10 a Hannun ICPC
- Wani makusancin tsohon gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana yadda abokinsa ya rika ribatar lokacin da hukumar ICPC ta ke tsare da shi
- An gano cewa tsohon gwamnan ya dukufa, inda kammala sauke Alƙur’ani mai tsarki tare da karanta littattafai 10 yayin da ya ke hannun hukuma
- Nasir El-Rufa'i na tsareva hannun ICPC, sai da an sako shi wucin gadi domin ya halarci jana'izar mahaifiyarsa tare da karban gaisuwa wajen makoki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna –Wani makusancin tsohon gwamnan jihar Kaduna ya bayyana yadda Nasir Ahmad El-Rufai ya yi amfani da lokacinsa a hannun hukuma.
Ya bayyana cewa El-Rufa'i bai yi asarar lokaci ba, domin ya yi amfani da lokacin da ya kwashe a tsare wajen ibada da karatu mai zurfi.

Source: Facebook
Mutumin, wanda aka bayyana da suna Bashir Garba Sufyan, ya wallafa a shafinsa na X cewa tsohon gwamnan ya maida hankali kan azumi, karatun Alƙur’ani da kuma bincike na ilimi.
Nasir El-Rufa'i ya koma gida
Daily Trust ta wallafa cewa Bashir Garba Sufyan ya kuma tabbatar da cewa tsohon gwamnan ya koma gida wajen iyalansa bayan hukumar ICPC ta sake shi na wucin gadi.
Ya ce:
“Alhamdulillah, Malam ya koma gida tare da iyalansa da abokansa. Abu na farko da ya gaya mana shi ne tun bayan da aka tsare shi yana azumi har zuwa jiya.”
Sufyan ya ƙara da cewa El-Rufai ya kammala karatun Alƙur’ani mai tsarki gaba ɗaya, ya karanta littattafai guda 10, sannan ya rubuta wasu littattafai a lokacin da yake tsare.
Yadda El-Rufa'i ya shiga hannun ICPC
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya shiga hannun ICPC tun a ranar 19 ga Fabrairu, 2026 bisa wasu zarge-zargen almundahana.
An kama shi ne bayan ya fito daga hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, inda aka yi masa tambayoyi na tsawon awanni 48.
Hukumar ICPC ta gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna bisa tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma halatta kuɗin haram.

Source: Twitter
Kotun ta ɗage sauraron buƙatar belinsa zuwa ranar 31 ga Maris. Sai dai, sa’o’i kaɗan bayan rasuwar mahaifiyarsa a birnin Cairo, hukumar ta yanke shawarar sake shi, duk da cewa ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa.
A halin yanzu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Kaduna Uba Sani da Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, sun aike da saƙonnin jajantawa ga El-Rufai a dalilin rasuwar mahaifiyarsa.
Ɗan El-Rufa'i ya kausasa harshe ga Uba Sani
A wani labarin, kun ji cewa a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026 aka sanar da rasuwar mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Wannan ta sa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya aika da sakon ta'aziyya ga El-Rufai kan rasuwar Hajiya Umma El-Rufai duk da akwai takun saka ta siyasa a tsakaninsu.
Sai dai, jim kadan bayan fitar da sakon ta'aziyyar, wani dan El-Rufai mai suna Bashir El-Rufai, ya yi masa martani mai zafi tare da bayyana cewa ba da son gaisuwar.
Asali: Legit.ng

