El Rufai Na Iya iya Samun Beli don Halartar Jana'izar Mahaifiyarsa? Lauya Ya Yi Bayani
- Hajiya Umma El-Rufai mahaifiyar tsohon gwamnan Kaduna ta rasu yayin da danta Nasir El-Rufai yake tsare a hannun hukumar ICPC
- Muhawara ta tashi a soshiyal midiya game da yiwuwar ko El-Rufai zai iya samun beli domin ya halarci jana'izar mahaifiyar tasa
- Barista Bashir Muhammad Bello ya fayyace abin da doka tace game da bada belin gaggawa ga wanda yake tsare don ya halarci jana'iza
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - A yau Juma'a, 27 ga watan Maris, 2026, Allah ya yi wa Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai rasuwa.
Malam Nasir El-Rufai na ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar ICPC bayan an gurfanar da shi gaban kotu, yayin da wannan babban rashi ya same shi.

Source: Twitter
Mahaifiyar Nasir El-Rufai ya riga mu gidan gaskiya
Hon. Bello El-Rufai, jika ga Hajiya Umma, kuma d'a ga El-Rufai ne ya sanar da rasuwar kakar tasu a sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook.
'Dan majalisar wakilan na mazabar Kaduna ta Arewa, ya sanar da cewa:
"Ina mai sanar da al'umma cewa kakata, Hajiya Umma El-Rufai ta rasu a yau. Ita ce mahaifiya ga mahaifinmu, Mallam Nasir El-Rufai.
"Muna matukar godiya ga Allah da irin rayuwar da ta yi, kuma muna rokonsa ya jikanta da Rahama. Allah ya jikan iyayenmu da muka rasa. Ni da iyalina, muna barar addu'o'inku. Na gode."
Muhawara kan ko El-Rufai zai samu beli
Jim kadan da fitar wannan sanarwa, muhawara ta balle a shafukan sada zumunta, game da yiwuwar ko Mallam Nasir El-Rufai zai iya samun beli don halartar jana'izar mahaifiyarsa.
Legit Hausa ta tuntubi kwararren lauya, Bashir Muhammad Bello, daga M.T Mohammed & Co. (Pinnicle Chambers) da ke jihar Kaduna, don jin ko doka ta ba El-Rufai damar halartar jana'izar mahaifiyarsa.
Barista Bashir ya ce wannan ba abu ne na yin muhawara a kansa ba, domin doka a bayyane take, cewa, mutuwar mahaifiya, mahaifi, miji, mata, ko wani makusanci ga wanda yake a tsare, yake fuskantar shari'a, ba ta cikin dalilin ba da beli.
Abin da doka ta ce kan belin El-Rufai
Matashin lauyan, ya yi karin bayani da cewa:
"Shi irin wannan, doka ta riga ta gudana a kan shi. Rashi na iyaye, ko 'yan uwa, ko d'a, ko wani abu da ke kusanci da wanda yake fuskantar shari'a, ba ya daga cikin dalilin ba da beli ko da kuwa na minti biyar ne.
"Dalilan da ke sanya wa a bayar da beli suna kunshe a cikin ACJL da ACJA, wanda mutuwa kuma ba ta ciki."
Sai dai, Barista Bashir ya ce akwai hanyar da El-Rufai zai iya samun beli, inda ya ce:
"Da yake shi beli gaba dayansa yana cikin wani abu ne da yake na ganin damar alkali, to idan alkali ya ga zai bada belin shi, saboda rashin da aka yi masa, to yana da dama, amma shi ma alkalin zai bada belin ne a kan abin da doka ta ce, kuma doka ba ta bada damar bada beli a kan rashi ba."

Source: Twitter
'Doka na yi komai kankantar laifi' - Bashir
Ko da aka tambaye shi game da yiwuwar a ba El-Rufai beli la'akari da cewar yanzu ne aka fara shari'ar tsohon gwamnan na Kaduna, har ma za a saurari bukatar belinsa a zaman kotu na ranar Litinin, Barista Bashir ya ce:
"Laifi ko na satar agwagwa ne, kai laifi ko na zagin wani ne, indai sunanshi laifi ne, wanda sai ka tsaya gaban kotu ta amsa laifi ko ka ki amsa laifi, sannan a nemi beli, to mutuwa ba ta a cikin dalilin da zai sanya a sake shi."
"Da ma a ce wanda ake karar ne yake rashin lafiya, to ko don gudun kada ya mutu, ana iya bada shi beli domin ya ga likita, amma wa don wani nasa ne ya mutu, to ba za a sake shi don ya je jana'iza ba."
- Barista Bashir Muhammad Bello.
Hukumar ICPC ta saki Nasir El-Rufai
A wani labari, mun ruwaito cewa, Bashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya wallafa na cewa an saki mahaifinsa, Malam Nasir El-Rufai.
Wannan sanarwa tana zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan rasuwar mahaifiyar tsohon gwamnan, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta riga mu gidan gaskiya a yau Juma'a.
Wani makusancin El-Rufai ya shaida cewa an saki tsohon gwamnan, kuma har ma ya riga ya bar ofishin hukumar ICPC, inda yake tsare tun Fabrairu.
Asali: Legit.ng
Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com
Bar. Bashir Muhammad Bello (Lawyer) Barr. Basheer Muhammad Bello (BMB) is one of the youngest barristers in the Nigerian Bar Association, Kaduna Branch. He works at M. T. Mohammed & Co. (Pinnacle Chambers).



