El Rufai Ya Yi Babban Rashi a Rayuwa, Mahaifiyarsa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, na ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar ICPC
- Yayin da El-Rufai ya ke a tsare, Allah cikin ikonsa ya kaddara rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai
- Dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Mohammed Bello El-Rufai, ya sanar da rasuwar kakar ta sa a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, rasuwa.
Mahaifiyar El-Rufai mai suna Hajiya Umma El-Rufai ta koma ga mahalicinta ne a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026.

Source: Twitter
Mahaifiyar El-Rufai ta rasu
Babban yaron El-Rufai kuma dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Mohammed Bello El-Rufai, ya sanar da rasuwarta a shafinsa na X a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026.
“Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un."
Ina son sanar da jama’a rasuwar Kakata, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta riga mu gidan gaskiya a sa’o’in da suka gabata. Ita ce mahaifiyar mahaifinmu, Mallam Nasir El-Rufai."
"Muna mika godiya ga Allah bisa rayuwar da ta yi, kuma muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi mata rahama. Allah Ya jikan iyayenmu da muka rasa. A madadin iyalanmu, muna neman addu'o'inku. Mun gode.”
Bello El-Rufai
El-Rufai na tsare mahaifiyarsa ta rasu
Rasuwar Hajiya Umma El-Rufai na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan na jihar Kaduna yake tsare.
Hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaƙa (ICPC) ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda 10 a gaban kotu.
ICPC ta gurfanar da El-Rufai ne kan tuhume-tuhumen da suka shafi zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma halatta kuɗin haram bayan ya shafe wata guda a tsare.
Ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, inda wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar belinsa zuwa ranar 31 ga watan Maris, 2026.
Alkalin kotun, mai shari'a, Rilwanu Aikawa, ya sanya ranar ne bayan ya saurari hujjoji daga ɓangaren wadanda ake kara da kuma na masu shigar da ƙara a ranar Talata, 24 ga watan Maris 2026.

Source: Facebook
An yi wa El-Rufai ta'aziyya
Tsohon sanatan Katsina ta Arewa, Ahmad Babba Kaita, ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Nasir El-Rufai.
A wani rubutu a shafinsa na Facebook, Ahmad Babba Kaita ya bayyana cewa:
"Allah ya isar wa malam Nasiru Ahmad Elrufa’i akan wanan bakar azzalumar gwamnatin da EFCC ICPC da DSS kan zaluncin da suke mashi."
"Allah Ya ji kan hajiya Ya sa ta huta Ya yi mata rahama."
Batun rasuwar uwargidan El-Rufai
A wani labarin kuma, an yada wasu rahotanni masu ikirarin cewa uwargidan Malam Nasir Ahmad El-Rufai ta rasu.
Hadiza Isma El-Rufai, ta fito fili ta ƙaryata wasu rahotanni da aka yaɗa a kafofin sada zumunta waɗanda ke iƙirarin cewa ta riga mu gidan gaskiya.
Rahotonya yi iƙirarin cewa "Aunty Safiya Ali Rufai," mahaifiyar ɗan majalisa Bello El-Rufai, ta rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Read molllllll
Asali: Legit.ng

