Gwamnan APC Ya Gana da Atiku don Kulla Shirin Kifar da Tinubu? Gaskiya Ta Yi Halinta

Gwamnan APC Ya Gana da Atiku don Kulla Shirin Kifar da Tinubu? Gaskiya Ta Yi Halinta

  • An yada wasu rahotanni masu nuna cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi wata ganawar sirri da Alhaji Atiku Abubakar a birnin Makkah na Saudiyya
  • A cewar rahotannin, gwamnan ya yi alkawarin ba da tallafin kudi domin nuna goyon baya ga yunkurin raba Shugaba Bola Tinubu da mulkin Najeriya a zaben 2028
  • Bayan bullar rahotannin, gwamnatin jihar Nasarawa ta fito ta yi gamsashshen bayani kan abin da aka yi ikirarin cewa ya faru

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Nasarawa - Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi martani kan rahotannin da ke cewa Gwamna Abdullahi Sule, ya gana da Atiku Abubakar.

Gwamnatin ta jihar Nasarawa ta musanta rahotannin da ke zargin cewa Gwamna Abdullahi Sule ya gudanar da wata ganawar sirri da Atiku Abubakar a birnin Makka na ƙasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Kano ya ga ta kansa, kotu ta shure rokon hana majalisa tsige shi

Gwamna Abdullahi Sule ya musanta ganawa da Atiku a Saudiyya
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Ibrahim Addra ya fitar, a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026.

Rahotannin dai sun ce Gwamna Sule ya gana da Atiku a lokacin gudanar da aikin Umarah, inda aka ce har ya yi alkawarin bayar da tallafin kuɗi domin marawa ƙoƙarin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 baya.

Wane martani gwamnatin Nasarawa ta yi?

Gwamnatin ta bayyana rahotannin a matsayin "ƙagaggun labaru, tsabagen ƙarya kuma abubuwan da ba su faru ba."

Sanarwar ta ce Gwamna Sule bai yi wata ganawa da Atiku ko na-kusa da shi ba yayin gudanar da ibadar, jaridar PM News ta kawo labarin.

Ta ƙara da cewa gwamnan ya sha amfani da kowace dama domin yaba wa salon shugabancin Shugaba Tinubu da kuma tabbatar da goyon bayansa ga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Gwamna Dauda APC, Matawalle ya kinkimo batun takara a 2027

Gwamnati ta nuna yatsa ga wasu 'yan siyasa

Gwamnatin ta zargi wasu ’yan siyasa da ƙoƙarin dagula kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Shugaba Tinubu da gwamnan, tana mai bayyana yaƙinin cewa wannan shirin ba zai yi nasara ba.

Sanarwar ta kuma nuna cewa mai.magana da yawun bakin Atiku, Paul Ibe, ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan kowace irin ganawa makamanciyar wannan.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce gwamnonin APC suna goyon bayan Bola Ahmed Tinubu ɗari bisa ɗari, tana mai jaddada cewa babu wani labarin ƙarya da zai iya shafar amincinsu gare shi.

Gwamna Sule ya musanta ganawa da Atiku
Gwamna Abdullahi Sule a wajen taron jam'iyyar APC Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Yaron Atiku ya yi murabus daga gwamnati

A wani labarin kuma, kun ji cewa Adamu Atiku Abubakar wanda yake matsayin bannan da ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishina a gwamnatin jihar Adamawa.

Murabus dinsa daga matsayin kwamishinan ayyuka da ci gaban makamashi ya kawo karshen shekaru bakwai da ya kwashe yana rike da wannan muhimmin matsayi, inda ya ajiye mukamin bayan sauya shekar Gwamna Ahmadu Fintiri.

Adamu Atiku ya ce samun damar ba da gudunmawa wajen bunkasa ababen more rayuwa da kuma fannin makamashi a Adamawa abu ne da ba zai manta da shi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng