An Dasa Bam a Sansanin Sojojin Amurka da ke Yaki da Iran

An Dasa Bam a Sansanin Sojojin Amurka da ke Yaki da Iran

  • An gurfanar da wani mutum da ya dasa bam a sansanin sojin Amurka da a yanzu haka ke jagorantar yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya da Iran
  • Rahoto ya nuna cewa babban lauyan gwamnatin Amurka ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris, 2026
  • Wata sanarwa ta nuna cewa gwamnatin Amurka ta yi karin bayani game da mutumin, inda ta ce a yanzu haka ya tsere zuwa kasar China neman mafaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - An tuhumi wani mutum da ya tsere zuwa China da laifin dasa bam da aka ƙera da hannu a wajen wani sansanin soji a jihar Florida.

An bayyana cewa wajen da aka dasa bam din nan ne hedikwatar sojojin US CC da ke jagorantar yaƙin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta tanadi dakaru miliyan 1 a shirin yin gaba da gaba da sojojin Amurka

Donald Trump da sojojin Amurka
Shugaba Donald Trump na yi wa sojojin Amurka bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An dasawa Sojojin Amurka bam

CNN ta wallafa cewa a yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis, babban lauyan gwamnatin Amurka a Florida ta Tsakiya, Gregory W. Kehoe, ya sanar da cewa an dasawa sojojin kasar bam.

Ya bayyana yadda masu bincike suka yi imanin cewa Alen Zheng ne ya dasa bam ɗin, da kuma yadda ‘yar uwarsa Ann Mary Zheng ta taimaka masa wajen ɓoye laifin da kuma tserewa zuwa China.

Kehoe ya ce har yanzu ba a samu wata shaida da ke nuna wata ƙasar waje na da hannu a lamarin ba, kuma ana ci gaba da bincike kan dalilan da suka sa Zheng ya aikata hakan.

Bayanin masu gabatar da kara

A cewar masu gabatar da ƙara, Zheng — wanda ya kira lambar gaggawa 911 ba tare da bayyana sunansa ba — ya yi kiran ne mintuna kaɗan bayan dasa bam ɗin a ranar 10 ga Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Lissafi na neman kwacewa: Trump na son gama yaki da Iran cikin gaggawa

A bayanan da suka yi, sun ce ya yi magana yana cewa akwai bam a sansanin sojin MacDill, amma bai bayyana inda bam ɗin yake ba.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump na yi wa Amurkawa bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yahoo News ta rahoto cewa an binciki sansanin amma ba a gano bam ɗin ba sai bayan kwanaki shida, a ranar 16 ga Maris, lokacin da aka same shi a wani wuri da ba a yawan zuwa a sansanin.

Bayanin jami'an tsaron Amurka

Jami’an tsaro sun ce bayan gwaji, an tabbatar bam ɗin na aiki, sai dai ba a bayyana dalilin da ya sa bai fashe ba har zuwa lokacin da aka gano shi.

A lokacin da aka gano bam ɗin, jami'an tsaro sun ce sun gano kayan haɗa bam a gidansa da kuma alamun bam ɗin a cikin motar da ya yi amfani da ita.

Iran za ta gwabza da sojojin Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Iran sun shirya gwabzawa da dakarun Amurka da ake hasashen Donald Trump zai iya turawa kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ke kara tura sojoji Gabas ta Tsakiya a shirin cigaba da yakin da ya kaddamar a Iran.

Duk da cewa Trump bai bayyana karara cewa zai tura sojojin kasa Iran ba, Tehran ta sanar da cewa tana saka ido a duk shirin da yake yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng