Turaki Ya Faɗa Matsala: Kotu Ta Bada Umarni a Kamo Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa
- Kotu ta bayar da umarnin kamo Kabiru Turaki saboda kin bayyana a gabanta kan tuhumar bayar da bayanan karya ga yan sanda
- Rundunar yan sanda na tuhumar shugaban jam'iyyar na PDP da laifin yaudarar hukuma a wata takardar koke da ya shigar a 2022
- A zaman shari'ar na yau, Mai Shari’a U.P. Kekemeke, ya ce Turaki ba shi da wani gamsasshen dalili na ƙin amsa sammacin kotu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Wata babbar kotu dake Abuja ta bayar da umarnin kamo Kabiru Tanimu Turaki, shugaban wani tsagi na jam’iyyar PDP a matakin kasa.
Kotu ta bayar da umarnin cafko shugaban jam'iyyar ne bayan ya gaza bayyana a gaban kotun a ranar Alhamis, 26 ga Maris, 2026.

Source: Twitter
Kotu ta bada umarnin kamo shugaban PDP

Kara karanta wannan
Tinubu: Arewa ta Tsakiya ta gama shiri, ta fitar da 'dan takarar Shugaban kasa a 2027
Alƙalin kotun, Mai Shari’a U.P. Kekemeke, ya bayyana cewa tsohon ministan ba shi da wani dalili na ƙwarai da zai sa ya ƙi amsa sammacin kotu, in ji rahoton The Cable.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya (IGP) ce ta shigar da ƙarar Turaki tana tuhumarsa da laifi guda ɗaya, wanda ya shafi zargin bayar da bayanan ƙarya ga hukumar ‘yan sanda a cikin wata takardar koke da ya rubuta tun a watan Oktobar shekarar 2022.
Wannan umarni na kama shugaban tsagin jam'iyyar ta PDP ya zo ne bayan da ya yi kunnen uwar shegu da zaman kotun na baya.
Neman sauya alkali a shari'ar shugaban PDP
Tun a zaman kotu na ranar 28 ga watan Janairu, aka tsara za a gurfanar da tsohon ministan, amma rashin halartarsa ya sa aka ɗage zaman.
A lokacin, lauyan wanda ake kara ya bayyana cewa wanda yake karewa bai zo kotun ba ne saboda sun rubuta wasiƙa ga babban alƙalin babbar kotun Abuja suna neman a canja alƙalin da ke sauraron shari’ar zuwa wani daban.
Jaridar The Nation ta ruwaito lauyan Turaki ya bayyana cewa sun shigar da koke ne saboda rashin amincewa da adalcin kotun ga wanda yake karewa wa.
Sai dai, Mai Shari’a K.N. Ogbonnaya, wanda ya taɓa zama a kan shari’ar, ya bayyana cewa:
“Shigar da koke ga babban alƙali ba zai iya dakatar da ci gaba da shari’ar manyan laifuffuka ba, sai dai idan umarni ya fito daga ofishin babban alƙalin.”

Source: Twitter
Hukuncin da kotu ta yanke yau
A zaman kotun na yau Alhamis, Mai Shari’a U.P. Kekemeke ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake wasa da lokacin kotu, inda aka bayyana cewa dole ne wanda ake tuhuma ya girmama doka.
Masu gabatar da ƙara sun jaddada cewa Turaki ya san da wannan zama amma ya zaɓi yin watsi da shi, in ji rahoton Vanguard.
Wannan takaddama dai tana zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP ke fama da rikicin cikin gida tsakanin tsatstsun dake takaddama kan shugabancin jam’iyyar na ƙasa.
Umarnin kama Turaki na nufin cewa jami’an tsaro suna da ikon kamo shi a duk inda yake domin tilasta masa bayyana a gaban kotu a zama na gaba.
PDP: Tsagin Turaki ya yi nasara a kotu
A wani labari, mun ruwaito cewa, kwamitin gudanarwa na PDP na kasa karkashin Kabiru Tanimu Turaki ya yi nasara a karar da aka shigar gaban babbar kotun Oyo.
A zaman yanke hukunci kan shari'ar, kotun ta tabbatar da sahihancin babban taron PDP na kasa da aka gudanar a Ibadan a kwanakin baya.
Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar PDP ke ci gaba da fuskantar rikice-rikicen cikin gida, wanda ke tilasta wa manyan jiga-jiganta sauya sheka.
Asali: Legit.ng

