DSS Ta Ceto Jami'in Gwamnatin Kano, Yan Ta'addan da Suka Sace Shi Sun Shigo Hannu

DSS Ta Ceto Jami'in Gwamnatin Kano, Yan Ta'addan da Suka Sace Shi Sun Shigo Hannu

  • Jami’an tsaron farin kaya ta DSS sun ceto sakataren ƙaramar hukuma da wasu 'yan ta'adda suka sace daga gidansa a Kano
  • Jam'an sun samu nasarar kama matasa biyu daga cikin wadanda ake zargi yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi
  • Masu garkuwar sun shiga gidan jami'in gwamnatin ana bikin Sallah, suka sace shi sannan suka nemi kuɗin fansar N300m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta samu nasarar ceto sakataren gudanarwa na ƙaramar hukumar Kibiya a jihar Kano, Alhaji Hamza Durya.

Wasu 'yan ta'adda da suka shiga garin da daddare a lokacin da ake bikin Sallah, suka yi gaba da shi tare da neman fana daga baya.

Kara karanta wannan

El Rufa'i na iya samun cikas, kotu ta gano babban kuskure a kararsa kan ICPC

Jami'an DSS sun ceto sakataren gudanarwa na Kano
Wasu daga cikin jami'an DSS a bakin aiki Hoto: DSS Unoffiial
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya tabbatar da ceto jami'in.

An ceto jami'in gwamnatin Kano

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa kwamishinan ya bayyana cewa jami’an DSS sun kaddamar da wani samame cikin gaggawa domin ceto jami'in da aka sace a makon jiya.

Ya ce jami’an sun nuna ƙwarewa wajen gudanar da aikin, inda suka kubutar da shi cikin ƙoshin lafiya ba tare da komai ya same shi ba.

Ya kara da bayyana cewa jami'an da suka kaddamar da aikin ceton sun kama mutane biyu da ake zargi, duk da cewa sun samu raunukan harbi yayin artabun.

Kara karanta wannan

Sojoji da 'yan sanda sun fada tarkon 'yan ta'adda, an rasa rayuka masu yawa

An kama wasu daga cikin wadanda suka sace jami'in gwamnati
Taswirar jihar Kano inda aka ceto jami'in gwamnati Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana wannan nasara a matsayin abin a yaba, tana mai cewa hakan ya nuna jajircewar jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Haka kuma ta jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf yana ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da kayan aiki da goyon baya domin inganta ayyukansu a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Bukatar gwamnati ga jama'ar Kano

An kuma bukaci al’umma da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu mai kama da shakku ga hukumomi, domin haɗin kai tsakanin jama’a da jami’an tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da laifuka.

Da yake bayani kan abin da ya faru da shi, Durya ya ce masu garkuwa da mutanen sun fara ne da tayar da ɗansa daga barci, inda suka tilasta masa ya nuna masu inda yake.

Kara karanta wannan

APC ta yi rashi a Kaduna, hadimin Gwamna ya sauya sheka zuwa ADC

Daga nan ne suka daure shi da sarƙa tare da rufe masa ido, suka kai shi wani ɗakin kaji da dabbobi a wani gari da ke kusa a ƙaramar hukumar Rano.

Ya ce a tsawon lokacin da yake hannunsu, ba ya ganin suna yin Sallah, sannan sun riƙa neman kuɗin fansa mai yawa.

A cewarsa, sun fara da neman Naira miliyan 300, daga baya suka rage zuwa miliyan 100, sannan suka sake dagewa kan adadin bayan sun ji cewa yana da kusanci da gwamnan Kano.

Durya ya kuma zargi cewa wani daga cikin makusantansa ne ya ba su bayanai, inda ya yaudare su cewa yana da kuɗi masu yawa. Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun fito ne daga Rijana a jihar Kaduna, yana mai godiya ga DSS bisa ceton rayuwarsa ba tare da an biya ko sisi ba. Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, mai suna Nasiru, ya amsa cewa sun fito daga Rijana ne domin aikata wannan ta’asa, kuma sun samu taimakon wasu masu ba su bayanai a cikin yankin. Ya ce su kusan mutum goma ne, amma yawancinsu sun tsere yayin artabu da jami’an tsaro, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbi.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da jami'an tsaro sun fafata ana shirin kama jagoran yan bindiga a Kano

An sace jami'in gwamnatin Kano

A baya, mun wallafa cewa wasu ƴan ta'adda aƙalla shida sun sace sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya, Hon. Hamza Musa Durba har gida.

Maharan sun kutsa kauyen a kan babura dauke da bindigu a makon da ya gabata inda suka shiga gidan jami'in gwamnatin, sai dai ba su harbi kowa ba a lokacin.

Rahotanni sun bayyana cewa duk da an sanar da ami'an tsaro, ƴan ta'addan sun yi gaggawar kammala abin da ya kai su, suka yi awon gaba da shi kafin dauki ya zo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng