Ana Zargin Ƴan Najeriya da Leƙen Asirin Amurka da Isra'ila domin Taimaka wa Iran

Ana Zargin Ƴan Najeriya da Leƙen Asirin Amurka da Isra'ila domin Taimaka wa Iran

  • Wani shaida na hukumar DSS, ya fadawa kotu cewa wasu da ake zargi da ta’addanci sun amsa laifin leken asiri
  • Mutumin ya tabbatar da cewa mutanen 3 sun yi leƙen asiri kan ofisoshin jakadancin Amurka da Isra’ila a yakin da ake yi
  • Ya ce wadanda ake tuhuma uku sun bayyana cewa sun je Iran domin samun horo kan makamai da tattara bayanan sirri kafin dawowa Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani mai ba da shaida a hukumar DSS ya bayyana yadda yan Najeriya ke leken asirin Amurka da Isra'ila.

James Simon ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa wasu mutane uku da ake zargi sun amsa laifin leƙen asiri kan ofisoshin jakadancin Amurka da Isra’ila.

DSS na zargin wasu yan Najeriya da leken asiri
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Sunayen yan Najeriya da ake zargi

Kara karanta wannan

A karshe, Trump ya samu kasashe 3 da za su taimaka ya shawo kan Iran

Ya ce wadanda ake tuhuma, Haruna Ali Abbas, Ibrahim Hussein Musa da Adam Suleiman, sun yi wannan furuci ne yayin bincike da kuma cikin rubutattun bayanansu bayan kama su, cewar Tribune.

Simon ya karanta bayanin Abbas inda ya amsa jagorantar tawagar zuwa Iran, inda aka horar da su kan sarrafa makamai da kuma tattara bayanan sirri.

A cewarsa, aikin da aka ba su ya hada da tattara bayanan bude ido game da Amurka da Isra’ila domin tura wa hukumomin Iran kamar yadda ya bayyana.

Ya kara da cewa Abbas ya ce manufar ita ce aika bayanai kan ofishin jakadancin Amurka da kuma na Isra’ila kamar yadda aka umarce su.

A yayin tambayoyi daga lauya wadanda ake zargi, Aliyu Yawuru, shaidan DSS ya dage cewa shiga irin wadannan ayyuka na leƙen asiri da daukar mutane aiki ta’addanci ne.

Simon ya kara bayani cewa aikin wadanda ake tuhuma ya hada da sa ido da tattara bayanai kan cibiyoyin jakadancin Amurka da Isra’ila a Najeriya.

Ya ce daya daga cikin bayanan da suka tattara ya nuna cewa gwamnatin Isra’ila ta ba gwamnatin Kwara tallafin noma a wani lokaci.

Kara karanta wannan

Pakistan za ta shiga tsakani a yakin Amurka da Isra'ila ke gwabzawa da Iran

Kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 1 ga Afrilu 2026 domin ci gaba da tambayar shaidar a karkashin binciken lauyoyin masu karewa.

Marigayi tsohon jagoran addini a Iran, Ali Khamenei, Bola Tinubu da Benjamin Netanyahu. Hoto: @khamenei_ir, Bayo Onanuga, Benjamin Netanyahu.

Source: Facebook

Zargin da ake yi wa Abbas

A cikin takardar tuhuma, an bayyana cewa an kama Abbas a ranar 16 ga Maris 2013 a filin jirgin saman Malam Aminu Kano yayin dawowarsa daga Lebanon.

Ana zargin sa da daukar matasa ‘yan Najeriya domin horon ta’addanci a Iran, tare da halartar tarukan ta’addanci da tallafa musu, cewar rahoton The Nation.

Su kuwa Musa da Suleiman ana tuhumar su da hada baki da shirya ayyukan ta’addanci ciki har da neman fasfo da bizar Iran domin samun horo.

Haka kuma ana zargin su da gudanar da leƙen asiri a Abuja da Kano da Lagos kan ofisoshin jakadancin Amurka da Isra’ila domin yiwuwar kai hari nan gaba.

Ukraine na zargin Rasha da taimakon Iran

An ji cewa shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy ya yi magana kan yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Zelenskiy ya ce kasarsa ta samu hujja karara cewa Rasha na bai wa Iran bayanan sirri, lamarin da zai kara tsawaita rikicin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban ya ce Rasha na amfani da fasahar tattara bayanan sigina da hadin gwiwa da wasu kasashen yankin domin taimaka wa Iran wajen kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.