Matatar Dangote Ta Fitar da Man Fetur zuwa Kasashen Afrika 5

Matatar Dangote Ta Fitar da Man Fetur zuwa Kasashen Afrika 5

  • Rikicin Gabas ta Tsakiya ya jawo an samu kalubale wajen samun kayayyakin makamashi a duniya
  • Matatar Dangote da ke jihar Legas a Najeriya ta fitar da tataccen man fetur zuwa kasashen nahiyar Afrika guda biyar
  • Tura man fetur din ya kasance lokaci na farko da matatar ta fara fitar da shi zuwa wajen tun bayan da ta kai matakin tace gangar danyen mai 650,000 a kowace rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Matatar man Dangote ta faɗaɗa tasirinta a yankin Afirka ta hanyar fitar da man fetur zuwa wasu kasashe.

Matatar Dangote ta fitar manyan jiragen ruwa na daukar kaya 12 ɗauke da tacaccen man fetur da nauyinsa ya kai tan 456,000 zuwa ƙasashe biyar na Afirka.

Matatar Dangote ta fitar da fetur zuwa kasashen waje
Motocin dakon man fetur a matatar Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta gano a ranar Lahadi, 22 ga watan Maris 2026 cewa an sayar da waɗannan kayayyaki ne ta hannun ’yan kasuwar duniya a ƙarƙashin tsarin "Free on Board" (FOB).

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar da Tinubu ya kulla da Turai ana tsakiyar yakin Amurka da Iran

An fitar da man fetur din ne a daidai lokacin da ake fama da ƙalubalen man fetur sakamakon rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Wadanne kasashe Dangote ya kai fetur?

Matatar ta tura man ne zuwa ƙasashen Côte d’Ivoire, Kamaru, Tanzaniya, Ghana, da Togo, wanda hakan ya nuna wani gagarumin ci gaba tun bayan da matatar ta kai matakin tace ganga 650,000 a kowace rana a watan Fabrairun 2026.

Wani babban jami’i a matatar, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da ikon yin magana da manema labarai, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin nuna ƙaruwar amincewa da ƙarfin tace man Najeriya da kuma sauyi a tsarin samar da mai a Afirka.

“Matatar man fetur ta Dangote ta ƙarfafa matsayin Najeriya a kasuwar makamashi ta yankin tare da nasarar sayar da jiragen ruwa 12 ta hannun ’yan kasuwa, waɗanda jimillar su ta kai tan 456,000 (456KT) na tacaccen man fetur."

- A cewar jami'in

Matatar Dangote ta kafa tarihi

Waɗannan kayayyaki da ’yan kasuwar suka tura zuwa ƙasashe irin su Côte d’Ivoire, Kamaru, Tanzaniya, Ghana, da Togo, su ne man fetur na farko da matatar ta fitar zuwa ƙasashen waje tun bayan samun ikon tace ganga 650,000 a rana a watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Matakin farko da alkali ya dauka a zaman shari'ar El Rufai da gwamnatin Najeriya

“An sayar da kayayyakin ne a ƙarƙashin tsarin FOB ga ’yan kasuwar duniya domin kai su waɗancan ƙasashe da aka bayyana."

- A cewar jami’in

Tasirin matatar Dangote na dada fadada

Jimillar tan 456,000 na tacaccen man fetur ya yi daidai da kusan lita miliyan 608, wanda hakan ke nuna girman waɗannan kayayyaki da kuma tasirin da za su iya yi wajen samar da mai a kasuwannin Afirka da dama, jaridar Premium Times ta kawo labarin.

Matatar Dangote ta fitar da fetur zuwa kasashen Afrika 5
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook
“Ta hanyar samar wa maƙwabta da sauran ƙasashe mai, ana sa ran matatar Dangote za ta ba da gudunmuwa wajen haɓaka tsaron makamashi a Yamma, Gabas, da Tsakiyar Afirka."
"Tare da rage jinkirin da ake samu a harkar sufuri da sayo mai daga ƙasashe masu nisa, rage tsadar farashi a kasuwannin man yankin ta hanyar sayo shi daga kusa, da kuma gina ƙwaƙƙwarar alaƙar kasuwanci tsakanin Najeriya da manyan ƙasashen Afirka."

- A cewar jami’in

Dangote ya magantu kan rikicin Gabas ta Tsakiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi tsokaci kan rikicin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Dangote ya gano matsalolin da yakin Amurka, Iran zai jefa 'yan Najeriya

Dangote ya yi gargadin cewa rikicin na iya tilasta wa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka sake ɗaukar matakan komawa yin aiki daga gida.

Attajirin ya nuna matsananciyar damuwa game da tasirin rikicin kan tattalin arziki da sauyin farashin mai ga nahiyar Afrika wadda ke fama da bashi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng