A Karshe, Trump Ya Samu Kasashe 3 da za Su Taimaka Ya Shawo kan Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump na cigaba da cewa yana tattaunawa da Iran domin ganin an samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya
- Duk da cewa Iran ta nuna ba ta tattauna da Donald Trump ba, Shugaban Amurka ya dage cewa akwai wadanda suka yi magana da shi
- A halin yanzu, wasu kasashen Musulmi guda uku da suka hada da Pakistan sun sanar da cewa za su iya jagorantar zaman sulhu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Kasashen Musulmi sun fara kokarin ganin cewa an kawo karshen yakin da aka fara a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila.
Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Donald Trump na cigaba da ikirarin cewa ya tattauna da shugabannin Iran amma su kuma suna cewa ba haka ba ne.

Source: Getty Images
Rahoton ABC ya bayyana cewa kasashen sun kara kaimi ne bayan Trump ya fitar da wasu sharuda 15 da ya ce yana so Iran ta cika su.
Kasashen da za su shiga tsakani
Kasashen Turkey, Egypt da Pakistan na jagorantar ƙoƙarin sasanta yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, yayin da yaƙin ke gab da shiga mako na huɗu.
Jaridar Washington Post ta ruwaito, tana mai danganta bayanan ga jami’an Amurka da na ƙasashen waje, cewa ƙasashen Gabas ta Tsakiya suna taka rawa a matsayin masu shiga tsakani a tattaunawar da ake fatan yi.
Rahoton ya bayyana cewa an yi ta yawan kiran waya tun daga ƙarshen mako zuwa ranar Talata, inda ƙasashen ke roƙon ɓangarorin biyu su kawo ƙarshen yaƙin.
Haka kuma ana kyautata zaton cewa Oman na cikin masu shiga tattaunawar, kasancewar a baya ta jagoranci tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka kafin ɓarkewar yaƙin.
Amurka/Iran: A ina za a tattuna?
Rahoton CNN ya nuna cewa Pakistan ta miƙa tayin karɓar bakuncin duk wata tattaunawa, inda majiyoyi suka ce akwai shirin gudanar da ganawa a Islamabad daga baya a wannan mako tsakanin Amurka da Iran.
Wasu bayanai sun nuna cewa ana sa ran Mataimakin shugaban Amurka JD Vance zai halarci zaman tattaunawar da ake tsammanin yi.

Source: Getty Images
Wasu majiyoyi biyu na cewa Amurka ta miƙa jerin buƙatu guda 15 ga Iran ta hannun Pakistan, amma ba a bayyana ko Tehran ta amince da ko daya daga cikinsu ba.
An ce ƙoƙarin diflomasiyya ya ƙaru ne bayan shugaba Donald Trump ya bai wa Iran wa’adin sa’o’i 48 da ta buɗe mashigar Hormuz amma ya janye daga baya.
Kim Jong Un ya gargadi Amurka
A wani labarin, kun ji cewa, Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya caccaki gwamnatin Amurka kan yakin da ta kaddamar a Iran.
Kim Jong Un ya bayyana haka ne yayin da ya jaddada cewa Koriya ta Arewa za ta cigaba da mallakar makaman nukiliya domin maganin makiya.
Shugaban ya gargadi Koriya da Kudu da cewa suna cikin manyan makiyan kasar shi, inda ya ce za su magance duk wata barazanar da za su fuskanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


