Akwai Kura: Dangote Ya Gano Matsalolin da Yakin Amurka, Iran Zai Jefa 'Yan Najeriya

Akwai Kura: Dangote Ya Gano Matsalolin da Yakin Amurka, Iran Zai Jefa 'Yan Najeriya

  • Yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya ya girgiza duniya ta hanyar kara farashin man fetur da iskar gas
  • Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ci gaba da rikicin 'yan Najeriya cikin matsala
  • Hamshakin attajirin ya nuna cewa idan ba tsayar da rikicin ba, tabbas 'yan Najeriya za su ji a jikinsu saboda matsalolin da za su biyo baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas- Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi gargadi kan rikicin da ake gudanarwa a Gabas ta Tsakiya.

Dangote ya yi gargadin cewa rikicin na iya tilasta wa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka sake ɗaukar matakan komawa yin aiki daga gida kamar na lokacin COVID idan ba a samu sassaucin rikicin ba.

Dangote ya yi magana kan rikicin Gabas ta Tsakiya
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Dangote ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Litinin, 23 ga watan Maris 2026 bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a gidansa da ke Ikoyi a Legas.

Kara karanta wannan

An bankado yadda gwamnati ta ba 'abokin Tinubu' kwangilar Naira tiriliyan 1.4

Wace matsala Dangote ya hango?

Attajirin ya nuna matsananciyar damuwa game da tasirin rikicin kan tattalin arziki da sauyin farashin mai ga nahiyar Afrika wadda ke fama da nauyin bashi.

“Idan wannan abun bai lafa ba, ku sani, yawancinmu a Afirka ba mu da wani babban tanadi."
“Sannan kuma, mutane yawanci fita suke su nemo kuɗin gobe ko ma na ranar. Wasunsu, idan ba su yi aiki a ranar ba, ba za su ci abinci ba.”

- Aliko Dangote

Dangote ya kafa misali

Ya kawo misali da matakin da ƙasar Indonesia ta ɗauka sakamakon matsin lamba na rikicin makamashi, inda hukumomi suka buƙaci ma’aikata su riƙa aiki kwanaki huɗu kawai a mako, kuma suna duba yiwuwar komawa tsarin aiki daga gida baki ɗaya kamar lokacin annobar COVID-19.

“A wasu ƙasashen a yau abin da suka yi shi ne, sun buƙaci kowa ya yi aiki daga gida saboda ba za su iya jurewa (tsadar sufuri da makamashi) ba."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da yakin Iran da Isra'ila, jirgin sama ya yi hatsari, sojoji sun mutu

“Ina jin ’yan Indonesia ma kwanaki huɗu kawai suke zuwa aiki a mako. Kuma za su duba yanayin, idan abubuwa ba su gyaru ba, za su buƙaci kowa ya daina fita aiki baki ɗaya."
“Za mu yi kamar lokacin COVID, inda mutane za su riƙa aiki daga gida."

- Aliko Dangote

Dangote ya gana da Shugaba Bola Tinubu
Aliko Dangote tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Wane gargadi Dangote ya yi?

Biloniyan ɗan kasuwar ya yi gargaɗin cewa Afirka za ta sha wahala kan rikicin da ba ta da hannu a cikinsa, jaridar Leadership ta kawo labarin.

“Ba batun makamashi kawai ba ne. Wasu mutanen za su yi ƙoƙarin amfani da damar su ce, ‘Ah, wannan dama ce. Don haka bari na nemi kuɗi.’"
“Don haka, idan wannan abun bai lafa ba, zai ci gaba da ruruwa yana yin sama, kuma gwamnatoci ba za su iya ƙara wa ma’aikata albashi ba da gaske. Saboda haka, mutane za su ji jiki sosai."

- Aliko Dangote

Dangote ya kara kudin man fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote da ke Legas ta sanar da kara kudin litar man fetur da take sayarwa ga 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Hadimin gwamna ya yanke jiki ya fadi, ya mutu a wurin taro

​A sakon da matatar ta aike wa abokan hulɗarta, ta sanar da su cewa ta ƙara farashin lita ɗaya daga ₦1,175 zuwa ₦1,245.

Baya ga ƙarin farashin lita, matatar ta kuma ƙara farashin samar da man ta hanyar ruwa daga ₦1,512,648 zuwa ₦1,606,518 a kan kowane tan ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng