An Fadi Jihar da za a Jigbe Jiragen Yakin Amurka a Arewacin Najeriya

An Fadi Jihar da za a Jigbe Jiragen Yakin Amurka a Arewacin Najeriya

  • Hedkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da isowar jirage marasa matuka zuwa kasar nan daga Amurka domin tallafawa dakarun soji
  • Rahotanni sun nuna cewa za a ajiye jirage marasa matukan a Arewacin Najeriya ne domin tattara bayanan 'yan ta'adda masu kai hari
  • Hakan na cikin yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da Amurka domin yaki da 'yan ta'adda tun bayan zargin kisan Kiristoci da aka yi a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Amurka ta jibge jiragen sama marasa matuka na MQ-9 Reaper da kuma sojoji 200 a Bauchi domin tallafa wa yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a Najeriya.

Matakin ya fi karkata kan tattara bayanan sirri, sa ido da kuma horas da sojoji, ba wai shiga yaki kai tsaye ba, tare da karfafa hadin gwiwa tsakanin sojojin Amurka da na Najeriya.

Kara karanta wannan

Yayin da ake yaki da Iran, jirgin sama ya yi hadari a kasar Amurka

Jirgin yaki maras matuki na Amurka
Jirgin yakin Amurka a wani taro a Faransa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Me Jiragen Amurka za su yi a Bauchi?

CNBC ta rahoto cewa jami’an Amurka da na Najeriya sun shaida cewa akwai jiragen MQ-9 da dama da ke aiki a kasar tare da sojoji 200, suna ba da horo da kuma bayanan sirri ga rundunar sojin Najeriya.

Sun bayyana cewa wadannan sojoji ba za su shiga cikin rundunonin da ke fagen daga kai tsaye ba, kuma jiragen ba su kai hare-haren sama, sai dai suna tattara bayanai ne kawai.

Daraktan yada labarai a hedkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya tabbatar da cewa Amurka na amfani da wasu kayan aiki daga filin jirgin sama na jihar Bauchi.

Ya ce:

“Wannan tallafi na kara inganta sabuwar cibiyar hada bayanan sirri tsakanin Amurka da Najeriya, wadda ke samar da bayanai masu amfani ga kwamandojin mu a fagen daga.”

Jiragen MQ-9, wadanda ake kira Reaper, na iya tashi sama na fiye da awa 27 suna sa ido, kuma ana iya amfani da su wajen tattara bayanai ko kai hari.

Kara karanta wannan

Trump ya juyo kan Najeriya, Amurka ta sake turo daruruwan sojoji, jiragen yaƙi ƙasar

Yaushe sojojin Amurka za su tafi?

Manjo Janar Uba ya bayyanawa Reuters cewa za a tantance tsawon lokacin da sojojin Amurka za su zauna a Najeriya ne bisa yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu.

Jibge sojojin Amurka da ya biyo bayan hare-haren sama da ta kai kan ‘yan ta’adda a Arewa maso yammacin Najeriya a karshen shekarar 2025, na nuna yadda Amurka ke sake shiga cikin yaki a kasashe.

Yadda jirgin yakin Amurka ke aiki a sama
Jirgin yaki samfurin MQ-9 Reaper a sama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A baya, Amurka na da wani sansanin jiragen sama marasa matuka a Nijar da kudinsa ya kai Dala miliyan 100 tare da sojoji kusan 1,000, inda suke sa ido kan ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

Amma an rufe shi a shekarar 2024 bayan gwamnatin sojan Nijar ta bukaci su fice, a wani mataki na kin amincewa da taimakon sojojin kasashen Yamma a yankin.

Denmark za ta gwabza da Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun kasar Denmark sun nuna cewa a shirye suke wajen tunkarar Amurka a shirin kwance tsibirin Greenland.

Kara karanta wannan

Trump zai sauya salon yaki da Iran, sojojin Amurka 2,500 sun nufi Gabas ta Tsakiya

A bayyana cewa sojojin sun fara taruwa a Greenland da makamai da suka hada da abubuwa masu fashewa domin kai hari kan dakarun Amurka.

Hakan na zuwa ne yayin da shugaba Donald Trump ke barazanar karbar yankin da ya ce yana da muhimmanci ga tsaron kasar shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng