Ana Ruguntsumin Sallah, 'Yan Bindiga Sun Kai Hari, an Sace Masu Ibada

Ana Ruguntsumin Sallah, 'Yan Bindiga Sun Kai Hari, an Sace Masu Ibada

  • An shiga fargaba bayan 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Tsagerun 'yan bindigan sun yi dirar mikiya a wata coci lokacin da ake tsaka da gudanar da ibada inda suka yi awon gaba da mutane
  • Jami'an tsaro sun kai daukin gaggawa bayan aukuwar lamarin, inda wasu majiyoyi suka ce an ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kwara, Najeriya - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kwara.

'Yan bindigan sun farmaki cocin ECWA da ke yankin Omugo, a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, inda suka yi awon gaba da wasu masu ibada.

'Yan bindiga sun sace mutane a Kwara
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa harin ya faru ne a safiyar ranar Lahadi, 22 ga watan Maris 2026 lokacin da ake gudanar da taron bauta na mako-mako.

Kara karanta wannan

Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya

'Yan bindiga sun sace masu ibada a coci

Harin 'yan bindigan ya haddasa fargaba a tsakanin masu ibada da mazauna yankin, jaridar Premium Times ta kawo labarin.

Sai dai, an ce haɗakar jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutane uku daga cikin waɗanda aka sace ɗin.

Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun afka cikin harabar cocin ne tare da sace mutane da dama kafin jami’an tsaro su kawo dauki.

Wata majiya daga ƙungiyar tsaro ta hadin gwiwa ta Kwara ta Kudu, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce aƙalla an sace mutane bakwai.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, kwamishiniyar yaɗa labarai ta jihar, Bolanle Olukoju, ta ce jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutane uku, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ganin an sako sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.

“Muna yaba wa jami’an tsaro, masu tsaron daji, da kuma ’yan banga na sa-kai kan martanin gaggawa da suka mayar cikin haɗin kai, wanda ya kai ga ceton mutane uku daga cikin waɗanda aka sace tare da taimakawa wajen fatattakar maharan.”

Kara karanta wannan

Rabon shinkafar Tinubu: Yadda ake 'bambance' Kudu da Arewa wajen tallafa wa mutane

- Bolanle Olukoju

'Yan bindiga sun kai hari a Kwara
Taswirar jihar Kwara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnati ta ba jami'an tsaro umarni

Olukoju ta ƙara da cewa gwamnati ta umarci hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen kamo waɗanda suka aikata hakan da kuma tabbatar da dawowar sauran mutanen cikin koshin lafiya.

“Yayin da muke yaba wa jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan martanin gaggawa, muna ba su umarnin tabbatar da cewa binciken da ake gudanarwa ya kai ga ceton sauran mutanen da kuma kamo masu laifin."

- Bolanle Olukoju

Haka kuma kwamishiniyar ta yi Allah-wadai da farmakar cibiyar addini da maharan suka yi, inda ta bayyana matakin a matsayin aikin matsorata kuma abin da ba za a amince da shi ba.

'Yan bindiga sun mutu a cikin kogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun gamu da ajalinsu yayin da suka yi kokarin tsallaka kogi a jihar Sokoto.

Akalla 'yan bindiga guda 150 ne suka mutu bayan wani jirgin ruwa da ke dauke da su ya kife a yankin Sabon Gida da ke Sokoto.

An ce ‘yan bindigan suna tafiya ne cikin adadi mai yawa lokacin da jirgin ya juye kwatsam, inda ya jefa dukkan wadanda ke ciki cikin ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com