Rabon Shinkafar Tinubu: Yadda Ake 'Bambance' Kudu da Arewa wajen Tallafa wa Mutane

Rabon Shinkafar Tinubu: Yadda Ake 'Bambance' Kudu da Arewa wajen Tallafa wa Mutane

A ranakun 14 zuwa 15 ga Maris, 2026, Shugaban Bola Tinubu ya umarci ƙungiyar 'Renewed Hope Ambassadors', da su rarraba shinkafa a faɗin ƙasar nan, ciki har da jihohin Arewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An gabatar da shirin raba abinci domin nuna tausayi ƙarƙashin manufar “Renewed Hope”, inda ake ba da tallafin abinci musamman na shinkafa da gaggawa a lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.

Yadda rabon shinkafa ya jawo maganganu a Arewa
Shugaba Bola Tinubuna Najeriya da shinkafa yar gwamnati. Hoto: Bayo Onanuga, Firdous Nazir/NurPhoto via Getty Images).
Source: Facebook

Bola Tinubu ya umarci raba shinkafa a Najeriya

Shugaban ya ba da umarnin ne yayin da al'ummar Musulmi suke azumin Ramadan, sannan yan uwansu Kiristoci ke na 'Lent', cewar Punch.

Duk da cewa hakan zai dan ba da taimako na ɗan lokaci, ya jawo muhawara a Arewa, inda yunwa mai tsanani ke addabar miliyoyin mutane.

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda na amfani da bidiyon azabtarwa don firgita al’umma": Masani ya bayar da mafita

Masu sukar shirin na cewa raba shinkafa wani mataki ne na siyasa na ɗan lokaci wanda bai magance tushen matsaloli ba kamar rashin tsaro, raguwar noma, da talauci.

Arewacin Najeriya na bukatar zuba jari mai dorewa a tsaro, noma, da samar da ayyukan yi fiye da irin wannan rarraba abinci na dan lokaci.

Abin da Arewa ta fi bukata a yanzu

Wani mai fashin baki kan lamuran yau da kullum, Barista Ibrahim Bello Kiyawa ya nuna damuwa kan rabon abinci a matsayin tallafi.

Kiyawa ya ce tun bayan shigowar wannan gwamnati, tana ta rabon shinkafa domin kula da walwalar mutane musamman a Arewa wanda hakki ne a samar masu da walwala.

Ya ce salon da ake bi duba da matsalolin da Arewa ke ciki na bayar da shinkafa da kayan masarufi amma kwata-kwata ba ita ba ce mafita saboda ba zai wadaci mutane ba.

"Abin takaici ne yadda ake raba shinkafa ga magidanta mudu daya ko biyu a matsayin tallafi, muna fama da matsalar tsaro wanda ya hana mutane noma, wannan lamari ya kawo koma baya.
"Madadin rabon shinkafa, a magance matsalar tsaro shi ne mafi muhimmanci, idan akwai tsaro mutane za su je gonaki su yi noma ba su bukatar shinkafa mudu daya ko biyu.

Kara karanta wannan

Ana shagulgulan Sallah, ƴan ta'adda sun sace jami'in gwamnatin jihar Kano

"Abu na biyu shi ne farfado da kasuwanci a Arewa musamman ga matasa saboda gudun bangar siyasa, bugu da kari ga lalacewar ilimi."

Matashin ya shawarci gwamnatoci su zage damtse wurin inganta ilimi da masana'antu saboda samun guraben ayyuka da gwamnati ba za ta iya ba jama'a aiki ba.

Cikakken bayani kan shirin rarraba shinkafa

Ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors (RHA), ƙarƙashin jagorancin gwamnan Imo, Hope Uzodimma, za ta gudanar da rarrabawar ta hanyar jihohi, ƙananan hukumomi da gundumomi domin tabbatar da gaskiya da isa ga jama’a.

Shirin ya shafi dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ake nufin musulmi da kiristoci a lokacin azumi.

Ba a bayyana jimillar buhunan shinkafar da za a rarraba ba a matakin ƙasa, sai dai misali ya nuna an ware buhu 1,200 ga jihar Niger.

Haka kuma, an danganta shirin kai tsaye da siyasa yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027, wanda ya janyo tambayoyi kan manufar siyasa a bayansa.

Arewa: Bukatun yankin ya fi na shinkafa

Jihohin Arewa musamman Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma) na fuskantar mummunar yunwa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gagarumar matsala ta tunkaro Isra'ila ana tsaka da yaki da Iran

Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) da FEWS NET sun yi hasashen cewa kusan ‘yan Najeriya miliyan 35 za su fuskanci matsananciyar yunwa a 2026, inda matsalar ta fi tsanani a Borno, Adamawa da Yobe.

Karin mutane miliyan 21 zuwa 22 za su bukaci agajin jin-ƙai a tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2026.

An yi ta magana kan rabon shinkafa a Kannywood
Nuhu Abdullahi da Alhassan Kwalle yayin rabon shinkafa a Kano. Hoto: Muktar Hassan.
Source: Facebook

Ce-ce-ku-ce kan rabon shinkafa a Arewa

Masu amfani da kafofin sadarwa da dama sun nuna damuwa game da bambanci a yadda ake yi a Arewa da kuma Kudu.

Hakan ya biyo bayan raba shinkafa da gwamnatin tarayya ta yi ta hannun daya daga cikin masu yada manufofin shugaban kasa a Arewa, Nuhu Abdullahi ga masana'antar Kannywood a Kano.

Wani mai amfani da Facebook, Jikan Oga ya ce abin takaici ne ana tallafawa yan Kudu da kayan sana'o'i amma a Arewa shinkafa kawai ake hada su da shi.

Ya ce:

"Kun ga yadda ake tallafawa mutane a Kudu ko, amma a Arewa an zo ana rabon shinkafa."

Wannan kwatance ya yi tasiri a kafofin sadarwa inda masu wasan barkwanci da dama suka rika yada lamarin domin kara jan hankulan yan Arewa da su hankalta.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

Haka kuma, Aminu J Town da ke daya daga cikin masu amfani da kafar sadarwa ya nuna takaici kan yadda aka raina wa Arewa hankali.

Aminu ya bayyana haka a wani bidiyo a Facebook inda ya caccaki wasu daga cikin wadanda suka karbi shinkafar duba da halin da yankin ke ciki.

Haka kuma, tun a baya, taimakon abinci da Seyi Tinubu ya raba a Arewa ya fuskanci suka mai zafi, ana kiransa “abincin titi” wanda ba ya dawo da mutunci.

Yawancin ‘yan Arewa na cewa wannan shiri yana ɓoye gazawar gwamnati maimakon magance ta.

Rabon shinkafa ya yi magana kan rabon shinkafa
Nuhu Abdullahi tare da Shehu Hassan Kano yayin rabon shinkafa a Kano. Hoto: Mukhtar Hassan.
Source: Facebook

An ba Tinubu shawara kan shigo da shinkafa

A baya, an ji cewa an bukaci Gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da shigo da shinkafa daga kasashen ketare.

Wani kwamitin manufofin noma da ke samun goyon bayan fadar shugaban kasa ya nuna damuwarsa kan adadin shinkafar da ke cikin Najeriya.

Ya ce alkaluman kasuwannin duniya sun nuna cewa 'yan Najeriya sun shigo da shinkafa sama da tan miliyan 2 kan makudan kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.