Yadda Rade Radin Mutuwar Netanyahu ke Karuwa duk da Bayyanar Shi a Bidiyo
- Jita-jitar mutuwar Benjamin Netanyahu ta yadu a kafafen sada zumunta bayan wani bidiyo da ya fito ya yi inda wasu ke zargin na bogi ne
- Firaministan Isra’ila ya yi kokarin karyata jita-jitar ta hanyar bayyana kansa a bidiyo, har ma ya yi barkwanci don tabbatar da cewa yana raye
- Sai dai hakan bai dakatar da masu amfani da kafafen sada zumunta ba, inda suka ci gaba da bincike da yada jita-jita kan cewa ya mutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra'ila - An garara karkatar da hankalin al'umma game da jita jitar mutuwar Firamininstan Isra'ila duk da cewa ya fito a wani bidiyo.
Maimakon bidiyon da Benjamin Netanyahu ya yi ya karyata jita-jitar, jama'a na cigaba da cewa bidiyon da fasahar AI aka yi shi kuma hakan ma dalili ne na cewa ya mutu.

Source: Getty Images
Tashar NBC ta hada wani rahoto na musamman kan yadda masu amfani da kafafen sadarwa ke nuna shakku kan rayuwar Netanyahu.
jita-jita kan mutuwar Banjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu ya yi kokarin karyata jita-jitar mutuwarsa da ta yadu a yanar gizo, amma wasu masu amfani da kafafen sada zumunta ba su gamsu ba.
Netanyahu ya zama abin magana kan wani ikirari da aka riga aka karyata amma har yanzu yana yawo cewa ya mutu a hare-haren Iran.
Masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara shakku kan lafiyar shugaban Isra’ilar bayan wani bidiyon jawabin da ya yi a talabijin ya fara yaduwa a makon da ya gabata, inda ya yi bayani kan yakin da ake yi da Iran.
Wasu jama'a sun yi zargin cewa bidiyon an kirkire shi ne da fasahar AI, suna cewa a wani lokaci hannun Netanyahu ya bayyana kamar yana da yatsu shida.
Da gaske Netanyahu ya fito da yatsa 6?

Kara karanta wannan
Shin da gaske an tafi da Mojtaba Khamenei zuwa Rasha don jinya? An ji gaskiyar zance
Shafin tantance bayanai na PolitiFact ya bayyana wannan ikirarin yatsu shida a matsayin karya, yana cewa akwai yiwuwar haske ne ya sa wani bangare na tafin hannunsa ya yi kama da karin yatsa.
Sai dai duk da haka, jita-jitar mutuwar Netanyahu ta ci gaba da yaduwa, inda masu amfani da TikTok da sauransu suka rika nazarin sakonnin da ya wallafa daga baya.
Barazanar kasar Iran ga Netanyahu
Netanyahu, mai shekaru 76, bai yawaita fitowa fili ba tun bayan fara yakin, musamman ganin cewa Iran ta sha alwashin kai masa hari kai tsaye a matsayin ramuwar gayya kan kisan Jagoranta, Ayatollah Ali Khamenei.
Mojtaba Khamenei, dan Ali Khamenei kuma sabon Jagoran koli na Iran, shi ma ba a gan shi a bainar jama’a ba tun bayan da Amurka ta fara yakin da kasar, kuma shi ma ana ta jita-jita kan lafiyarsa.

Source: Getty Images
Rashin lafiyar Netanyahu a baya
Duk da babu wata shaida da ke nuna cewa Netanyahu ba shi da lafiya a yanzu, lafiyarsa ta taba zama abin damuwa a siyasar Isra’ila.
Rahotanni sun nuna cewa Firaministan ya fuskanci matsalolin lafiya a baya, musamman bayan tiyatar gaggawa da aka yi masa a zuciya a 2023, da kuma tiyatar mafitsara a 2024.
An ce Netanyahu ya mutu
A wani labarin, kun ji cewa wani dan jaridar kasar Amurka, Nathan Levins ya yi ikirarin cewa Benjamin Netanyahu ya dade da mutuwa.
A wani bayani da ya yi, Levins ya bayyana cewa tun ranar 8 ga watan Maris, 2026 Benjamin Netanyahu ya rigamu gidan gaskiya.
Ya kara da cewa dan Firaministan ya shafe kwana bakwai yana zaman makokin rasa mahaifinsa kafin da dawo wallafa sakonni a kafar X.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

